Babban Jigon PDP Ya Fadi Jihohin da Atiku Ba Zai Samu Nasara Ba Tare da Dalilai

Babban Jigon PDP Ya Fadi Jihohin da Atiku Ba Zai Samu Nasara Ba Tare da Dalilai

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama a Najeriya ya yi hasashen abinda ya kira makomar Atiku Abubakar a zaben 2023
  • Osita Chidoka ya ce da yuwuwar Atiku ba zai kai labari ba a kudu maso kudu da kudu maso gabas, amma kuri'unsu ba zasu sauya komai ba
  • Babban jigon jam'iyyar adawa watau PDP ya ce duk ɗan takarar da ya samu nasara a arewa maso yamma da arewa maso gabas shi zai ci zaɓe

A ranar Lahadi 22 ga watan Janairu, 2023, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya ce shiyyoyin arewa maso yamma da arewa maso gabas ne zasu yanke wanda zai lashe zaben shugaban kasa.

Mista Chidoka, jigo a babbar jam'iyyar adawa PDP ya bayyana cewa kuri'un kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya ba zasu yi wani tasiri ba a zaɓen, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Atiku Ya Ambato Jihohin da PDP Za Ta Lashe ko Ta Doke APC

Atiku Abubakar.
Babban Jigon PDP Ya Fadi Jihohin da Atiku Ba Zai Samu Nasara Ba Tare da Dalilai Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A cewarsa, zakaran zaben 2015 da 2019, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai samu galaba a koda jiha ɗaya daga cikin jihohin shiyyon kudun guda biyu ba.

Osita ya ce ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, haifaffen kudu maso gabas, ya ɗauki matakin da ya dace na barin PDP, wanda a cewarsa tana taƙama da shiyyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bana tunanin Obi zai samu nasara - Chidoka

Tsohon ministan, wanda ya yi jawabi a cikin shirin Channels tv Sunday Politics, ya bayyana cewa Kabilar Ibo ta zuba jari mai girma a PDP amma duk da haka aka hana ta tikitin shugaban ƙasa.

Chdioka ya yi bayanin cewa gwabzawar tsakanin APC ne da PDP, inda a bayanansa ya nuna cewa mai yuwuwa Obi ya sha kaye.

Meyasa Atiku ba zai samu nasarar a shiyyoyin 2 ba?

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Baiwa Yan Najeriya Zabi, Ya Tono Wata Yaudara da Buhari Ya Yi a 2019

Da yake miƙa wuya cewa Atiku ba zai tabuka abin a zo a gani ba a Kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya, Chidoka ya ce:

"Buhari ya zama shugaban kasa ba tare da samun nasara a shiyyoyin biyu ba kuma haka ne zata sake faruwa a zaɓe na gaba. PDP zata zo na biyu a jihohin Oyo, Ekiti, Anambra, Abiya, Imo da Osun."
"Duk wanda ya lashe kuri'un arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa."

A wani labarin kuma Shugaban kasa Buhari ya sake magana kan alkawarin da ɗauka kafin ya hau kan madafun iko

Buhari ya kawo karshen kace-nace kan alƙawurran da ya ɗauka yayin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Bauchi ranar Litinin.

A cewar shugaban kasan, ya karaɗe kananan hukumomin Najeriya baki ɗaya a 2015 kana ya ziyarci jihohi 36 a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel