An Fitar Da Sunayen Jihohi 10 Da Buhari Zai Halarci Kamfen Din Tinubu Da Kansa

An Fitar Da Sunayen Jihohi 10 Da Buhari Zai Halarci Kamfen Din Tinubu Da Kansa

  • Kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, PCC, ta ce Shugaba Buhari zai halarci kamfen a jihohi a kalla goma
  • Hakan na zuwa ne a yayin da wasu yan adawa ke zargin da alamun shugaban kasar ba ya bawa dan takarar shugaban kasa Bola Tinubu goyon bayan da ya kamata tunda ba ya halartar kamfen dinsa
  • PCC ta ce ayyuka ne suka yi wa Shugaba Buhari yawa amma yana tare da Tinubu da jam'iyya dari bisa dari kuma zai halarci kamfen din da za a yi a jihohi a kalla 10 da suka hada da Adamawa, Yobe, Rivers, Katsina, Nasarawa, Ogun ds

Jam'iyyar APC ta ce shugaba Muhammadu Buhari a shirye ya ke ya halarci wasu tarukan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasarta da kansa nan gaba, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan Kano, Tinubu ya dura wata jiha domin tallata aniyarsa ta gaje Buhari

A cikin sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, Direktan watsa labarai kuma babban kakakin kwamitin kamfen din Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, SAN, ne ya fadi hakan a jadawalin kamfen da aka fitar a baya-bayan nan, ya ce shugaban kasar zai halarci kamfe a jihohi a kalla goma.

Buhari da Tinubu
An Fitar Da Sunayen Jihohi 10 Da Buhari Zai Halarci Kamfen Din Tinubu Da Kansa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Keyamo, wanda shine karamin ministan ayyuka da kwadago, ya ce Buhari a shirye ya ke ya halarci kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC.

Jihohin da ake sa ran Buhari zai halarci kamfen din Tinubu

Wani sashi na cikin sanarwar ya ce:

"Idan za a iya tunawa, Shugaban Kasa duk da ayyuka sosai da ya ke da shi, ya halarci kaddamar da kamfen din dan takarar shugaban kasa a Jos ranar 15 ga watan Nuwamban 2022. Bayan ya amince ya zama ciyaman din kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami’an DSS Sun Kama Kwamandan ISWAP da ya Dasa Bama Ranar da Buhari zai Sauka Kogi

"A jadawalin da aka fitar jiya (5 ga watan Janairun 2023) shugaban kasa zai halarci kamfen a kalla a jihohi goma.
"Jihohin sune Adamawa a ranar 9 ga watan Janairu; Yobe a ranar 10 ga watan Janairu; Sokoto a ranar 16 ga watan Janairu; Kwara a ranar 17 ga watan Janairu; Ogun a ranar 25 ga watan Janairu; Cross Rivers a ranr 30 ga watan Janairu; Nassarawa a ranar 4 ga watan Fabrairu; Katsina a ranar 6 ga watan Febrairu; Imo a ranar 14 ga watan Fabrairu da na karshe Jihar Lagos State a ranar 18 ga watan Fabrairu."

Sanarwar ta cigaba da cewa PCC na son mika godiyarta ga Shugaba Buhari shugaban jam'iyya bisa jagorancinsa na gari da lokacin da ya ware don tattara kan yan jam'iyya da magoya baya.

An kuma yi kira ga yan jam'iyya da masoya su fito kwansu da kwarkwata kamar yadda suka saba don halartar ralli din don cimma nasara da izinin Allah.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

Ganduje: Arewa ba ta da uzurin da zai sa ba za ta zabi Bola Tinubu ba

A wani rahoton, Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ce mutanen arewa ba su da wani uzurin da zai sa ba za su zabi dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a 2023.

Ganduje ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel