Ganduje: Dalilin Da Yasa Arewa Ba Ta Da Wani Uzuri Sai Dai Ta Zabi Tinubu

Ganduje: Dalilin Da Yasa Arewa Ba Ta Da Wani Uzuri Sai Dai Ta Zabi Tinubu

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zaburar da yan arewa kan goyon bayan Bola Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress, APC
  • Ganduje ya ce Tinubu ya bada muhimmin gudunmawa wurin cigaban dimokradiyya da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari don haka lokacin sakayya ya yi
  • Gwamnan na Kano da ke daf da kammala wa'adinsa na biyu ya kuma ce bai taba ganin wani mahaluki da ya fi son arewa fiye da Tinubu ba

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce arewa ba ta da wani uzuri illa ta mara wa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu baya, kuma ta jefa masa kuri'u.

A cewarsa, Tinubu ya yi sadaukarwa sosai don kafuwar dimokradiyya da cigabanta a Najeriya, musamman wurin kokarin tallafawa yan arewa, don haka lokacin sakayya ya yi, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tinubu ya fasa kwai kan ganawa da gwamnonin G-5, ya ce akwai lauje cikin nadi

Gwamna Ganduje
Ganduje: Dalilin Da Yasa Arewa Ba Ta Da Wani Uzuri Sai Dai Ta Zabi Tinubu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ganduje ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya halarci wani taron kungiyar magoya baya mai suna 'Volunteers for Democracy' karkashin jagorancin sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji da aka yi a filin wasa na Sani Abacha.

Ban taba ganin mai son yan arewa kamar Tinubu ba - Ganduje

Ya ce:

"Arewa da yan arewa ba su da uzuri illa su goyi bayan Tinubu kuma su zabi jam'iyyar APC. Bola Ahmed Tinubu ya daka rawar gani sosai yayin da kuma ya taimakawa yan arewa da cigaban Najeriya. Don haka, lokacin sakayya ya yi.
"Tinubu ya mara wa Shugaba Buhari baya har sai da ya zama shugaban kasa. Bai nemi a bashi wata mukami na siyasa ba kuma ya cigaba da goyon bayan gwamnati. Ban taba ganin mai kaunar arewa kamar shi ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Mutanen yankin su Yakubu Dogara sun juya masa maya sun rungumi Bola Tinubu

A gefe guda, mutanen yankunan Tafawa Balewa/Bogoro/Dass da ke jihar Bauchi sun fito sun nuna goyon bayansu ga takarar Bola Tinubu da sauran yan takarar APC a jihar.

Mutanen yankunan da Yakubu Dogora, tsohon kakakin majalisar tarayya ke wakilta sun sha banban da ra'ayinsa na adawa da tikitin musulmi da musulmi na APC.

Sun bayyana cewa za su mara wa Tinubu baya ne saboda ayyuka da tsare-tsare da ya kawo a jihar Legas lokacin yana gwamna, suna son ya maimaita a matakin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel