Jami’an SSS Sun Damke ‘Dan T’addan da Ya Dasa Bam a Kogi Kafin Zuwan Buhari

Jami’an SSS Sun Damke ‘Dan T’addan da Ya Dasa Bam a Kogi Kafin Zuwan Buhari

  • Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS sun bayyana damke wanI kwamandan Boko Haram da ake zargi da dasa bam a Kogi ranar da Buhari ya je jihar
  • Ba a nan Otaru ya tsaya ba, yana da hannu wurin kai farmaki caji ofis, balle gidan gyaran hali na Kuje tare da sauran miyagun lamurra a yankin
  • Afunanya, kakakin DSS ya bayyana cewa, ana cigaba da bin cikar Otaru kuma za a gurfanar da shi gaban kuliya nan babu dadewa

Kogi - Wanda ake zargi da saka bam a jihar Kogi a ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ke kai ziyara jihar, ya shiga hannun jami’an tsaro.

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta sanar da kamen a wata takarda da kakakinta Peter Afunanya ya fitar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

Premium Times ta rahoto yadda bam ya tashi a ranar Alhamis kusa da fadar Ohinoyi na kasar Ibira, mintoci kadan kafin zuwan Buhari jihar kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar.

A kalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a tashi bam din a yankin Karaworo dake karamar hukumar Adavi ta jihar.

A takardar da ta fitar a ranar Laraba, SSS tace bam din an saka shi ne a wani abun hawa.

Kamar yadda wata takarda da ta fita ranar Laraba daga Peter Afunanya, kakakin DSS, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Abdulmumin Ibrahim Otaru, wani shugaban ISWAP da wani Saidu Suleiman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta ruwaito yadda wani abu mai fashewa ya tashi a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi a ranar 29 ga watan Disamba, 2022.

Lamarin, wanda ya auku jim kadan kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu kwangiloli a jihar, ya auku a wani masallaci kusa da fadar Ado Ibrahim, sarkin kasar Ebira.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta Aike wa da Ƙani Gidan Maza Kan Soyayya da Matar Aure

Haka zalika, Afunanya ya bayyana yadda Otaru ke da alhakin sauran hare-hare, duk da balle gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022.

"Yayin cigaba da bincike ya bayyana yadda Otaru wanda babban shugaban ISWAP ne, ko dai ya shirya ko kuma yake da alhakin kai mummunan harin: Harin 24 ga watan Yuli, 2022 a rundunar 'yan sandan Najeriya, Eika- Ohizenyi na karamar hukumar Okene dake jihar Kogi.
“Inda wani sifetan 'yan sanda, Idris Musa, ya rasa ransa, sannan aka yi awon gaba da bindiga 2 kirar AK47 a harin; harin 5 ga watan Yuli, 2022 na gidan yarin Kuje a yankin Kuje na FCT; da na 5 ga watan Agusta, 2022 a kamfanin kera tayin na yammacin Afirka (WACL) a karamar hukumar Ajaokuta da ke Kogi, inda aka yi garkuwa da indiyawa uku.”

- Kamar yadda takardar ta bayyana.

"Idan za a tuna mutane biyar, duk da wani ba Indiye daya, 'yan sanda biyu da direbobin kamfanin biyu suka rasa rayukansu a harin. An saki wadanda aka yi garkuwa dasu a 31 ga watan Agusta, 2022.

Kara karanta wannan

Kaico: Tashin hankali yayin da mai siyar da fetur ya babbake abokinsa a kan cajar waya

"Otaru ya kai farmaki inda aka sakaya 'yan ta'addan da kuma wuraren jihar Kogi. Haka zalika, shi da tawagarsa sun jagoranci farmaki da dama na garkuwa da mutane a Kogi da jihar Ondo. Sai dai, wadanda ake zargin sun shiga hannu, kuma za a gurfanar dasu bada dadewa ba.”

- Ya cigaba da cewa.

An saka bam a Kogi, sa’o’i kadan kafin saukar Buhari

A wani labari na daban, wani abu mai fashewa ya tashi a kusa da fadar Sarkin Ibira a jihar Kogi.

Lamarin ya auku ne ana sauran sa’o’i kadan da kafin saukar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar don kaddamar da wasu muhimman ayyuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel