Gwamnan PDP Na Tsaka Mai Wuya, Zai Iya Rasa Kujerar sa Saboda Rigima da Atiku

Gwamnan PDP Na Tsaka Mai Wuya, Zai Iya Rasa Kujerar sa Saboda Rigima da Atiku

  • Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde na cikin tsaka mai wuya saboda rigimar da yake yi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP
  • Gwamnan na fuskantar barazanar rasa kujerar sa idan bai yi hattara ba saboda yaɗda siyasar jihar sa take
  • Nasarar kowane ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa, na iya sanyawa gwamnan yayi bankwana da tazarcen da yake nema

Tazarcen da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo yake nema na fuskantar barazana daga cigaba da nacin da tawagar gwamnonin G5 suke yi na ganin sun juyawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, baya.

Seyi Makinde shine kaɗai gwamnan da yake kan wa'adin sa na farko a cikin ƴan tawagar ta G5.

Makinde
Gwamnan PDP Na Tsaka Mai Wuya, Zai Iya Rasa Kujerar sa Saboda Rigima da Atiku
Asali: Twitter

Duk da cewa Ortom, Ugwuanyi da Ikpeazu suna neman kujerar Sanatoci, Makinde ya fisu fuskantar barazana duba da irin yadda siyasar jihar Oyo take. Rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Faɗi Gaskiya Kan Dan Takarar Da G-5 Ta Kulla Yarjejeniya da Shi

Siyasar jihar Oyo tana a ƙarƙashin jiga-jigai da yawa masu ƙarfin faɗa a ji ta yadda ba wanda shi kaɗai zai iya yin iko kan wanda zai lashe zaɓe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jiga-jigan PDP a Oyo Suna Tare da Atiku

Duk da haƙiƙancewar Makinde na ƙin goyawa Atiku baya, wasu manyan ƴan jam'iyyar PDP a jihar, ciki har da tsohon ministan haƙar ma'adanai, Dr Wole Oyelese, na tare da Atiku.

Haka zalika tsohon ministan birnin tarayya Abuja, Chief Olajumoke Akinjide, ya aygana goyon bayan ga tsohon mataimakin shugaban kasa.

Wani mazaunin birnin Ibadan mai sharhi kan lamarin siyasa, Rasheed Olanrewaju, ya bayyana cewa idan ba ayi taka tsan-tsan ba jam'iyyar adawa na iya amfani da rikicin PDP ta amshe jihar.

"Yakamata Seyi da masu bashi shawara su sake yin nazari. Lamari ne mai sarƙaƙiya. Idan Tinubu yaci zaɓe, APC zata samu tagomashi a jihar."

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Ya Yi Wani Abin Ban Mamaki, Ya Sace Zuciyar 'Yan Najeriya da Dama

"Musamman yadda shugabannin PDP magoya bayan Atiku za su iya juya wa gwamnan baya domin ramuwa kan abinda yayi musu."
"Idan Atiku yaci zaɓe ba tare da goyon bayan Makinde ba, nan ma akwai sarƙaƙiya, saboda ɗan takarar APC, Teslim Folarin, yana da alaƙa mai kyau da wasu jagororin PDP wacce yake a cikinta har 2017. "
"Saboda haka za su iya mara masa baya ta hanyar yin jarjeniyar cewa zai dawo jam'iyyar bayan zaɓe domin ganin PDP ta cigaba da riƙe jihar. Wasu ƙusoshin PDP tuni har sun fara masa yaƙin neman zaɓe. Inji shi."

PDP: Sabon Bayani Ya Fito Yayin Da Gwamna Ortom Ya Magantu Kan Yarjejeniyar Da Aka Ce G5 Ta Yi Da Tinubu

Gwaman jihar Benuwai, Samuel Ortom yayi watsi da raɗe-raɗen da aka yaɗawa cewa tawagar su ta G5 ta cimma yarjejeniya da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Babban Jigon Siyasa Ya Bayyana Abinda Ka Iya Faruwa da APC, Tinubu a Zaben 2023

Gwamnan yana ɗaya daga cikin gwamnonin PDP waɗanda basa ga maciji da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel