PDP: Sabon Bayani Ya Fito Yayin Da Gwamna Ortom Ya Magantu Kan Yarjejeniyar Da Aka Ce G5 Ta Yi Da Tinubu

PDP: Sabon Bayani Ya Fito Yayin Da Gwamna Ortom Ya Magantu Kan Yarjejeniyar Da Aka Ce G5 Ta Yi Da Tinubu

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi watsi da hasashen da ake yi na cewa gwamnonin G5 sun yi yarjejeniya da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu
  • A baya-bayan nan rahotanni sun karade kafafen watsa labarai da ke cewa Tinubu da gwamnonin biyar da ke fushi da PDP sun cimma yarjejeniya
  • Ortom, wanda mamba ne na gwamnonin na G5, amma, ya ce rahotannin ba gaskiya bane, yana mai cewa kungiyar za ta sanar da yan Najeriya idan ta dauki mataki

London, UK - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce gwamnonin G5 ba su riga sun cimma wata yarjejeniya da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ba, a zaben 2023.

Hakan ya ci karo da rahotanni daban-daban a kafafen watsa labarai da suka fito a ranar Alhamis, 30 ga watan Disamba da ke nuna cewa gwamnonin na G5 sun yi wata yarjejeniya da dan takarar shugaban kasar na APC.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5

Tinubu da Ortom
PDP: Sabon Bayani Ya Fito Yayin Da Gwamna Ortom Ya Magantu Kan Yarjejeniyar Da Aka Ce G-5 Ta Yi Da Tinubu. Hoto: Benue State Government, Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Gwamna Ortom ya yi watsi da ikirarin yin yarjejeniyar da Tinubu a lokacin da aka tuntube shi a ranar Alhamis.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce idan aka yi la'akari da gogewarsu, idan sun yi wata yarjejeniya, sune za su fito da kansu su fada wa yan Najeriya.

Gwamnan na Benue yayin da ya ke bada amsa kan tambayar da aka masa na yarda su goyi bayan Tinubu ya ce:

"Ba gaskiya bane. Babu wani abu mai kama da haka. Da gogewarmu, idan za mu yi wani abu, za mu sanar da al'umma."

Ortom mamba ne na G5, gwamnonin jam'iyyar PDP biyar da suka yanke shawarar ba za su mara wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar baya ba saboda rikicin cikin gida na jam'iyyar da ba a warware ba.

Kara karanta wannan

Ganawar sirri: Daga karshe bayani ya fito bayan ganawar Tinubu da gwamnonin PDP 5 a Landan

Tambuwal: Jami'iyyar PDP Za Ta Dauki Mataki Kan Wike A Lokacin Da Ya Dace

A yayin da ake ta yada jita-jita kan dan takarar shugaban kasa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers zai goyi baya a 2023, takwararsa na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ja kunensa.

A martaninsa, Tambuwal ya ce babu wanda ya fi karfin jam'iyya kuma tana da ikon hukunta duk wanda ya saba dokokinta.

Tambuwal ya aike da jan kunne ga Wike da sauran gwamnonin PDP hudu da ke fushi da jam'iyyar, Channels TV ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel