Wike Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa, Ya Bayyana Gaskiya Kan Halin Da G5 Ke Ciki

Wike Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa, Ya Bayyana Gaskiya Kan Halin Da G5 Ke Ciki

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana gaskiya kan raɗe-raɗen da ake yaɗawa cewa tawagar su ta G5 ta cimma yarjejeniya wani ɗan takara
  • Gwamnan yace har yanzu babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da suka cimma yarjejeniya da shi saɓanin abinda ake yaɗawa
  • Gwamna Wike yace duk abinda ke faruwa yanzu somin taɓi ne na daga cikin babbar rigimar da zata biyo baya nan gaɓa kaɗan

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa tawagar gwamnonin G5 na jam'iyyar PDP, ba su cimma wata yarjejeniya ba da wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a zaɓe mai zuwa na 2023. 

Nyesom Wike.
Wike Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa, Ya Bayyana Gaskiya Kan Halin Da G5 Ke Ciki Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya bayyana hakan ne a lokacin buɗe fara aikin ginin titin hanyar Eneka-Igbo Etche a birnin Fatakwal a ranar Juma'a. Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Rigima Da Atiku Zata Sanya Gwamnan PDP Ya Rasa Kujerar Sa

A kalaman sa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sun ce Wike yayi hira da BBC inda yace mun yi jarjejeniya da wane da wane. Babu bidiyo ko sautin murya, amma wasun ku sun ɓata lokacin su suna sauraren waɗannan surutan."
"Baku san cewa idan ina son yin wani abu ba, zan yi shi? Baku sani ba? Kuna buƙatar kuyi jita-jita? Baku buƙatar yin jita-jita. Sunce akwai rigima amma babu wata rigima."
"Abinda yake faruwa yanzu somin taɓi ne kawai kafin zuwan rigimar dake tafe nan gaba."
"Saboda haka mutane na, ina son gaya muku cewa duk hukuncin da zan yanke, zan sanar da ku. Ba zan iya yanke wani hukunci ba ba tare da yin shawara.da ku ba. A cewar gwamnan."

A ruwayar Channels tv, gwamna Wike ya zargi Atiku da ganawa da wasu gwamnonin APC a ɓoye kuma ya gaza cika alkawarinsa na adalci da daidaito a PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Tona Asirin 'Yan Siyasar Dake Jin Haushin Shigo da Na'urar BVAS a Zaben 2023

Gwamnan PDP Na Tsaka Mai Wuya, Zai Iya Rasa Kujerar sa Saboda Rigima da Atiku

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Oyo na fuskantar barazanar rasa kujerar sa saboda rikicin da yake yi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Gwamna Seyi Makinde yana ɗaya daga cikin gwamnonin G5 waɗanda ke takun saka da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar.

Makinde shine kaɗai daga cikin gwamnonin mai neman tazarce a babban zaɓe mai zuwa 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel