Hawaye Da Alhini Yayin Da Jigon Jam'iyyar APC Ya Mutu A Hadarin Mota

Hawaye Da Alhini Yayin Da Jigon Jam'iyyar APC Ya Mutu A Hadarin Mota

  • Honarabul Abdullahi Kanti, jagoran kamfen din dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Taraba ya rasu
  • Kanti ya rasu ne a ranar Talata, 27 ga watan Disamban 2022 sakamakon hadarin mota a Lau Road a hanyarsa na zuwa Jalingo
  • Sanata Emmanuel Bwacha, dan takarar gwamnan APC a jihar Taraba ya yi alhinin rasuwar Kanti, ya yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama

Jihar Taraba - Honarabul Abdullahi Kanti, jagoran kamfen din gwamna na dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a karamar hukumar Karim Lamido na jihar Taraba ya rasu.

Tribune ta rahoto cewa Kanti ya mutu ne a hadarin mota a ranar Talata, 27 ga watan Disamba a kan hanyar Lau Road yayin da ya ke hanyarsa na zuwa Jalingo, jihar Taraba.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu

Yan APC
Hawaye Da Alhini Yayin Da Jigon Jam'iyyar APC Ya Mutu A Hadarin Mota. Hoto: APC Vanguard.
Asali: Depositphotos

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta kwamitin yakin neman zaben gwamna na Bwacha (BGCC) ta fitar, a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba ta ce an dauke gawarsa an kai Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Jalingo.

Sanarwar na dauke da sa hannun Aaron Artimes, sakataren watsa labarai na kamfen din karamar hukumar kuma aka fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba.

Mutuwar Kanti: Dan takarar gwamnan APC a Taraba ya yi martani

Da ya ke martani kan labarin mutuwar Kanti, dan takarar gwamna na APC a Taraba, Sanata Emmanuel Bwacha ya ce wannan babban rashi ne a wurinsa, rahoton Daily Post.

Bwacha ya ce ya san marigayin sosai kuma sun shaku ne bayan an zabe su a majalisar dokokin jihar Taraba a 1998.

Ya kuma ce kwamitin kamfen dinsa za ta yi kewan nagartaccen dan siyasa kuma mutumin kirki mai son zaman lafiya, ya yi addu'a Allah ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Dau Alkawarin Gina Masallaci da Coci a Wani Kauye

Za a yi jana'izar marigayi Honarabul Kanti a ranar Asabar, 31 ga watan Disamban 2022, bisa koyarwar addinin kirista.

Zaben 2023: Jigon APC Osita Okechukwu ya ce Peter Obi ne ke tayarwa Tinubu hankali

Osita Okechukwu, jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya ce Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ne kawai zai iya fito na fito da Bola Tinubu.

Osita ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi dashi a shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel