Jam'iyar PDP Zata Gyara Dukkan Abubuwan da APC Ta Bata, Okowa

Jam'iyar PDP Zata Gyara Dukkan Abubuwan da APC Ta Bata, Okowa

  • Abokin gamin ɗan takarar shugaban kasa na PDP yace jam'iyyarsu ta zo ne ta gyara barnar da APC ta tafka a Najeriya
  • Tsohon dan takarar gwamna da mambobin APC sama da 500 sun sauya sheka zuwa PDP a wurin kamfe a jihar Delta
  • Gwamna Okowa yace APC ta kawo koma baya a bangarori da dama kamar ilimi, tattalin arziki da sauransu

Delta - Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta kuma abokin takarar Atiku a inuwar PDP yace jam'iyyarsu ta zaburo ne ta gyara ɓarnar da jam'iyyar APC ta tafka wa 'yan Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto Okowa na cewa mutanen jihar Delta ba su bukatar mutum mai alfahari ya karbi ragamar shugabanci a zaɓen 2023.

Gwamna Okowa a wurin kamfe.
Jam'iyar PDP Zata Gyara Dukkan Abubuwan da APC Ta Bata, Okowa Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a garin Ughelli, ƙaramar hukumar Ughelli yayin gangamin yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Delta a inuwar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Ɗau Dumi, Yace Zai Zuba Dukiyarsa a Caca Kan APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'u Ba a 2023

Jiga-jigan APC sun koma PDP

A wurin kamfen ne, tsohon dan takara wanda ya nemi tikitin gwamna a inuwar APC, Chief Osiobe Okotie, da mambobi sama da 500 suka sauya sheka zuwa PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka, gwamna Okowa ya sake jagorantar jirgin kamfen zuwa Oleh dake ƙaramar hukumar Isoko, inda ya ce:

"Jam'iyar APC ta rusa tattalin arziki da jami'o'in Najeriya da rashin tsaron da suka zo da shi ga kuma yajin ASUU ya ƙi karewa. ASUU ta shiga yajin aiki ana tsaka da karatu a jami'o'in Delta."
"PDP zata kawo waraka ga dukkan matsalolin da APC ta kawo wa 'yan Najeriya. A Delta bamu son gwamna mai alfahari da jiji da kai wanda ba ya ganin girman mutane."
"Irin waɗan nan gurbatattun abubuwan da sauransu ne PDP ta fito domin canza canji a 2023. PDP ta ga abunda muke wa mutanen Delta ne ya sa ta bamu matsayin mataimakin shugaban kasa, nan gaba zamu karbi saman."

Kara karanta wannan

'Yan Takara Biyu a 2023, Shugabanni da Kusoshin Jam'iyyar NNPP Sun Koma APC a Jihar Arewa

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Fallasa Asirin Yan Siyasan Da Basu Son Amfani da BVAS a 2023

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Gombe yace babu mai jin tsoron na'urar BVAS sai wanda ya san bai tabuka wa mutane komai ba

Da yake kamfen a yankin Garko, gwamna Inuwa Yahaya yace a shirye yake ko yau a fita runfunan kaɗa kuri'a domin yana da masoya.

Gwamna yana cikin gwamnonin APC a shiyyar arewa maso gabas dake kokarin zarce wa a kan kujerunsu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel