Zaben 2023: Sabon Matsala Ga Tinubu A Yayin Da PDP Ta Fada Wa Yan Najeriya Abinda Ta Gano Kan APC
- Jam'iyyar PDP ta ce APC ba ta da hangen nesa kuma tana jagorantar yan Najeriya zuwa wurin da ba ta sani ba
- Kola Ologbandiyan, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa ne ya yi wannan zargin a safiyar ranar Laraba da safe
- Ologbondiyan, yayin da ya ke barazana ga nasarar Tinubu na APC a zaben 2023, ya ce jam'iyyar mai mulki tana jagorantar yan Najeriya zuwa wurin da ba su sani ba kuma sun gano hakan
Kwamitin kamfen na jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC tana jagorantar yan Najeriya zuwa wurin da ba ta sani ba.
Wannan sabon jawabin daga bangaren Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP, barazana ne ga Bola Tinubu na jam'iyyar APC a babban zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kola Ologbondiyan, kakakin kwamitin yakin neman zaben PDP, PCC, ya yi wannan jawabn ne a ranar Laraba da safiyar 28 ga watan Disamba ya bayyana hakan a shirin Sunrise Daily na Channels Television.
Abin da ke faruwa a baya-bayan nan game da PDP, APC, Bola Tinubu, Atiku Abubakar, zaben 2023
Ologbondiyan ya ce duk nisar da mutum ya yi a tafiya ta hanyar da ba dai-dai bane, da zarar ya gane, zai juya, ya kara da cewa yan Najeriya sun gano cewa ba kan hanyar dai-dai suke ba saboda zaben APC.
Ya ce:
"Za ka iya zama mai hangen nesa ne kawai idan kana samun cigaba. A halin da jam'iyyar APC ta dauki kasar mu zuwa tafiyar da bata san inda za ta tafi ba, ba za mu iya barin makomarmu a hannunsu ba."
2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu
Kalli bidiyon a kasa:
Wannan jawabin na zuwan ne daga bangaren Atiku a PDP a lokacin da wani rahoto ya ce wasu gwamnoni na shirin barin Atiku su koma bangaren Bola Tinubu na APC.
PDP ta tsinduma cikin rikici tun bayan da Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar hamayyar kan kiran ga daidaito, adalci a shugabancin jam'iyyar.
Babban jigo a jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a Jihar Sokoto
A wani rahoton, Alhaji Yushau Kebbe, wani babban jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Sokoto, a ranar Juma'a ya koma jam'iyyar APC.
Kebbe ya bayyana hakan ne yayin wata jawabin da ya yi wa manema labarai a Sokoto, yana mai cewar rashin jagoranci na gari ne yasa ya dauki matakin.
Daga cikin dalilansa, ya kuma zargi PDP ta Sokoto da gaza samar da ababen more rayuwa ga mutanen jihar.
Asali: Legit.ng