Buhari Ya Hadu da Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Sa Ba a Ganin sa Wajen Yi wa APC Kamfe

Buhari Ya Hadu da Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Sa Ba a Ganin sa Wajen Yi wa APC Kamfe

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawa da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Haduwar ta su ta zo bayan Buhari ya ce zai goyi ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa na APC a 2023
  • Shugaban na Najeriya ya yi alkawarin taya Tinubu kamfe, amma ya ce dole zai fi ba aikin ofishinsa karfi

Abuja - ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa a inuwar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock a Abuja.

Kafin haduwarsu, an ji Malam Garba Shehu a shafin Twitter yana tabbatar da cewa mai gidansa, Muhammadu Buhari yana tare da Bola Tinubu.

Mai magana da yawun bakin shugaban na Najeriya ya yi watsi da zargin da wasu ke yi na cewa shugaban kasa bai goyon bayan takarar Tinubu.

Kara karanta wannan

Osinbajo Ya ba Marada Kunya, a Karon Farko Tun da Aka Shiga Kamfe, Ya Ziyarci Tinubu

Shugaban kasar ya tabbatarwa Asiwaju Bola Tinubu mai neman gaje kujerar shi a 2023, a shirya yake da ya taya shi yakin neman shugabanci.

The Cable ta rahoto Buhari yana cewa aikin ofishinsa ne yake hana shi ya fita kamfe, akasin abin da wasu ke rayawa na rashin goyon bayansa.

Buhari da Tinubu
Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Abuja Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Garba Shehu

“Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa APC da ‘yan takaransu a zaben shekara mai zuwa cewa a shirya yake a kullum, ya yi wa ‘dan takaransu na shugaban kasa da sauran ‘yan takara kamfe da cikakken karfi da imaninsa.
Hakan domin watsi da damuwar da wasu suka yi na cewa shugaban kasar bai taba fita kamfe ba tun da aka kaddamar da yakin neman zabe a garin Jos a jihar Filato, kuma ya jaddada yana siyasa, amma zai fi maida hankali ga aikinsa.”

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Adadin Kujerun Da Jam'iyyar APC Za Ta Lashe

Buhari zai tallata APC a 2023

A jawabinsa, Shehu ya ce Mai girma shugaban kasa da ya je birnin Washington DC a Amurka, ya fadawa jama’a lallai zai taya jam’iyyarsa kamfe.

Muhammadu Buhari yana da ra’ayin a ‘yan shekarun bayan nan, babu wata jam’iyya da ta dage wajen yakin neman zabe a Najeriya kamar APC.

Buhari yana ganin jam’iyyarsu ta APC ta bar ‘yan adawa a baya, kuma wannan ya sa yake sa ran ‘yan takaransu za su samu kyakkyawar nasara.

Osinbajo da Tinubu ana tare

Daidai lokacin da wasu ke cewa Yemi Osinbajo bai goyon bayan tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima, sai ga rahoto cewa ya kai masu ziyara.

Bola Tinubu mai neman mulkin Najeriya a APC ya yi bayanin abin da tattaunawar shi da Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Osinbajo ta kunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel