Sabon Bidiyon Tinubu Yana Kwasar Rawa Bayan Taron Landan, El-Rufai ya Taya shi

Sabon Bidiyon Tinubu Yana Kwasar Rawa Bayan Taron Landan, El-Rufai ya Taya shi

  • Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, ya girgije tare da rausayawa cike da nishadi bayan taron Gidan Chatham da suka kammala a Landan
  • A bidiyon dake fallasa cewa liyafar cin abincin dare ce aka hada tare da mukarrabansa wadanda suka hada da fitattun gwamnoni, an sako sautin waka
  • Babu jimawa wakar ta ratsa mai fatan zaman shugaban Najeriyan inda ya motsa tare da girgijewa, lamarin da yasa har da Gwamna El-Rufai aka taya shi rawan

Landan - Sabon bidiyon Bola Ahmed Tinubu, ’dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, yana kwasar rawa cike da nishadi ya ba jama’a mamaki.

Tinubu yan rausayawa
Sabon Bidiyon Tinubu Yana Kwasar Rawa Bayan Taron Landan, El-Rufai ya Taya shi. Hoto daga @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Bidiyon dai ya bayyana ne bayan taron da yayi tare da jawabi kan manufofinsa a Gidan Chatham dake birnin Landan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abokin Takarar Peter Obi Ya Yi Garumin Zargi A Kan Tinubu

Tinubu tare da rakiyar mukarrabansa da suka hada da gwamnoni tare da gogaggun ‘yan siyasa sun dira birnin Landan din cikin ranakun karshen mako domin yin taron.

Cike kuwa da nishadi da jin dadin nasarar kammala taron, Tinubu da sauran ‘yan siyasan sun zauna liyafar cin abincin dare wacce aka kure sauti a wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bai yi kasa a guiwa ba, ya tashi tsaye daga kujerar da yake zaune tare da rausayawa inda babu jimawa Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna tare da sauran suka taya shi.

An saki fitacciyar wakar mawakin nan na kudancin Najeriya mai suna Kizz Daniel wacce ya saka wa suna ‘Buga’.

Alamu na nuna babu shakka wakar ‘Buga’ ta buga tare da ratsa zuciyar ‘dan siyasan wanda ya kasa daurewa sai da buga rawansa na musamman.

Kara karanta wannan

Amimu ya shaki iskar 'yanci: Yadda aka mika matashin ga iyayensa daga magarkama

Bidiyon Tinubu yana rawa

A wani bidiyon na daban, an ga ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zage yana kwasar rawa a cikin wani taro da mata.

A bidiyon da shugaban hukumar NURTW, MC Oluomo ya fitar, ya kwatanta Bola Tinubu da mutum mai karfi da jini a jika, hakan yasa yake kwasar rawa cike da nishadi.

MC Oluomo ya kara da cewa, Yana tsaye gyam a bayan Tinubu inda yake goyon bayan kudirinsa na mulkar Najeriya tare da yin nasarar lashe zaben 2023 dake gabatowa babu dadewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel