2023: Abinda Jam'iyyar APC Zata Yi Ta Lashe Babban Zabe Mai Zuwa, Buhari

2023: Abinda Jam'iyyar APC Zata Yi Ta Lashe Babban Zabe Mai Zuwa, Buhari

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana abu ɗaya da jam'iyyar APC zata yi don samun nasara a babban zaɓen 2023
  • Ɗan takarar gwamnan Katsina a inuwar APC, Dikko Radda, da abokin takararsa, Faruk Lawal Jobe, sun ziyarci Buhari a Daura
  • Buhari ya ƙara jaddada aniyarsa na tabbatar da sahihi kuma gamsasshen zaɓe a shekara mai kamawa

Daura, Katsina - Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shawarci jam'iyyar APC cewa haɗin kai a tsakanin 'ya'yanta ne babban ginshiƙin da zai kai jam'iyyar ga nasara a zaben 2023.

Shugaban ƙasan yace zaman tsintsiya ɗaya da kuma haɗa guiwa da juna ne matakin nasara a ko wane irin zaɓe, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari a Daura.
2023: Abinda Jam'iyyar APC Zata Yi Ta Lashe Babban Zabe Mai Zuwa, Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya yi wannan furucin ne a mahaifarsa, Daura ranar Jumu'a lokacin da ya karɓi bakuncin Dakta Dikko Radda, ɗan takarar gwamnan Katsina a inuwar APC.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Arewa Ya Tiƙa Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari

Dakta Radda ya kaiwa shugaban ƙasa ziyara har gidansa tare da abokin takararsa, Faruk Lawal Joɓe, ranar Jumu'a 9 ga watan Disamba, 2022.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari yace akwai bukatar shugabannin jam'iyya, "Su zauna a inuwa ɗaya" domin su kange duk wata barazanar raba kawunansu kuma su dunkule don guje wa rashin nasara a zaɓe.

Shugaban ya ƙara da cewa ya samu labarin yadda yakin neman zaɓe ke tafiya gunin sha'awa a Katsina kuma ya ji daɗi ganin yadda aka dage da jajircewa a kamfen.

Ina nan kan bakata na gudanar da sahihin zaɓe - Buhari

Bugu da ƙari yayin wannan ziyara, Buhari ya jaddada wa 'yan takarar cewa yana nan kan bakarsa na ba da fili ga kowa a gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa sakamakon zaɓen gwamna a jihohin Ekiti da Osun sun isa shaida da zata tabbatar da kudirinsa game da zaɓe, kamr yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Cikar Kwari Yayin Da Masari Ya Mika Tuta Ga Ɗan Takarar Gwamnan Katsina a 2023

Daga karshe ya gaya wa Radda da Jobe cewa ya ji daɗin ziyarar da suka kawo masa kana ya yi wa jam'iyyar APC fatan samun galaba a zaɓe mai zuwa.

APC Ta Samu Gagarumin Goyon Baya a Gombe

A wani labarin kuma Tsohon Mataimakin Gwamna, Shugaban Matasan PDP Na Shiyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Jam'iyyar APC ya karbi jiga-jigan masu sauya sheƙa daga PDP a wurin ganganin fara yaƙin neman ta zarcen gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.

Manyan jiga-jigan sun ce sun gwammaci su rungumi zahirin abinda suke gani a ƙasa fiye da alƙawurran ɗa jam'iyyar PDP ta ɗaukar masu na iska.

Asali: Legit.ng

Online view pixel