Hotunan Tsofaffin Zakarun Super Eagles a Kano don Yakin Zaben Tinubu/Shettima

Hotunan Tsofaffin Zakarun Super Eagles a Kano don Yakin Zaben Tinubu/Shettima

  • Tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa na kungiyar Najeriya ta Super Eagles, sun dira jihar Kano domin gangamin yakin neman zaben Bola Tinubu
  • Daga cikin tsofaffin zakuran akwai Daniel Amokachi, Taribo West, Emmanuel Babayaro, Peter Rufai, Victor Ikpeba da sauransu
  • Mai masaukinsu, Baffa Babba Danagundi, ya bayyana cewa zamansu a Kano zai kasance musu abun tunawa a yayin da zasu fara gangamin yakin zaben Tinubu da Shettima

Kano - A kalla tsofaffin zakarun kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles 27 ne suka isa birnin Kano domin kaddamar da gangamin yakin neman zaben Tinubu da Shettima wanda za a yi a filin wasa na Sani Abacha.

Amokachi and Co
Hotunan Tsofaffin Zakarun Super Eagles a Kano don Yakin Zaben Tinubu/Shettima. Hotuna daga TheCable.ng
Asali: UGC

Tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafan sun samu tarba ta musamman a jihar a ranar Juma’a daga Baffa Baba Danagundi, tsohon ‘dan majalisar jihar Kano, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jaji, Jigon Jam’iyyar APC a Zamfara Ya Ba Tawagar Kamfen din Tinub Kyautar Motoci 70

A yayin jawabi ga manema labarai, Danagundi yayi alkawarin tabbatar da zaman tsofaffin ‘yan kwallon a jihar mai dadi kuma abun tunawa a yayin da zasu fara gangamin kamfen din goyon bayan Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.

Tinubu shi ne ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 dake gabatowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin ‘yan wasan Super Eagles din dake Kano don gangamin sun hada da Daniel Amokachi, Peter Rufai, Victor Ikpeba, Julius Aghahowa, Mutiu Adepoju, Taribo West da Emmanuel Babayaro da sauransu.

Ga wasu daga cikin hotunansu:

Kano Tinubu
Hotunan Tsofaffin Zakarun Super Eagles a Kano don Yakin Zaben Tinubu/Shettima. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kano Tinubu
Hotunan Tsofaffin Zakarun Super Eagles a Kano don Yakin Zaben Tinubu/Shettima. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kano Tinubu
Hotunan Tsofaffin Zakarun Super Eagles a Kano don Yakin Zaben Tinubu/Shettima. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Mutane da dama sun fadi yayin gangamin mutum miliyan 1 na Tinubu a Kano

A wani labari na daban, a cikin watan Nuwamban da ya gabata ne shugaban hukumar KAROTA na jihar Kano, Baffa Babba Danagundi, ya shirya gangamin mutum miliyan daya don ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Fito da Lakanin da APC Za Tayi Amfani da Shi, a Doke PDP, LP da NNPP

Legit.ng Hausa ta zagaya ta wurin gidan gwamnati zuwa asibitin Abdullahi Wase wanda aka fi sani da asibitin Nasarawa inda da safiya ta ga tsaro ya tsananta.

Jami’an tsaro da suka hada da jami’an KAROTa sun fito aiki don gyara titunan da za a wuce.

Mutun 23 ne suka yanke jiki suka fadi yayin gangamin da ya tara matasa da magoya bayan Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel