Zamfara: Jigon APC ya Gwangwaje Tawagar Kamfen din Tinubu da Motoci 70

Zamfara: Jigon APC ya Gwangwaje Tawagar Kamfen din Tinubu da Motoci 70

  • Aminu Sani Jaji, jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya raba motoci saba’in a kananan hukumomi goma sha hudu na jihar Zamfara
  • Ya rabo motocin ne domin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima na jam’iyyar APC a zaben 2023
  • Duk da Jaji yace yana da yakinin cewa APC zata yi nasarar lashe zabukan 2023 yace Tinubu yana da gogewa ta kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

Zamfara - Daraktan kamfen din Tinubu na yankin arewa maso yamma, Aminu Sani Jaji, ya bayar da gudumawar ababen hawa 70 ga kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara domin inganta yakin neman zaben ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu/Shettima
Zamfara: Jirgin APC ya Gwangwaje Tawagar Kamfen din Tinubu da Motoci 70. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Anyi rabon ne a ranar Talata yayin kaddamar da kamfen din Jajiwna gida-gida na majalisar wakilai mazabar Kaura Namoda/ Birnin Magaji ta tarayya wanda aka yi a filin wasa na Kaura Namoda, jaridar Leadership ta rahoto.

Yayi jawabi ga magoya bayan jam’iyyar da masu ruwa da tsakin APC, Jaji yace wannan kyautatawar tana daga cikin gudumawarsa kan kamfen din Asiwaju da Shettima.

“Mun zo nan ne domin kaddamar da kamfen din mu a matsayin gudumawarmu ta tabbatar da nasarar Tinubu/Shettima da APC baki daya.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Takardar da ofishin yada labaran Jaji ta Abuja ta fitar a ranar Laraba tace.

Ya kwatanta Tinubu matsayin ‘dan siyasa mai gogewa da zai iya shawo kan matsalar tsaro da kalubalen tattalin arziki kuma zai kai Najeriya matakin cigaba, jaridar Blueprint ta rahoto.

Jaji yayi kira ga masu kada kuri’a da su goyi bayan APC tare da zabar Tinubu/Shettima da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a jihar, duk da ya bayyana cewa yana da yakinin APC zata yi nasara a zabukan 2023 masu zuwa.

APC zata Kaddamar da manhajar tallafin kamfen din Tinubu da Shettima

A wani labari na daban, Kwamitin kamfen din jam'iyyar APC na kasa zaI kaddamar da manhajar tara kudin tallafi ga 'yan takarar ta na shugabancin kasa.

Za a kaddamar da wannan manhaja ne a cibiyar Civil Centre da ke titin Ozumba a yankin Victoria Island da ke birnin Legas da misalin karfe 11 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel