Angulu da Kan Zabo: Sanatan PDP Yana Rokon Matasa da Su Zabi Tinubu

Angulu da Kan Zabo: Sanatan PDP Yana Rokon Matasa da Su Zabi Tinubu

  • Sanata Chimaroke Nnamani na jam’iyyar PDP ya roki matasan Najeriya da su zabi Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC
  • A takardar da Nnamani ya fitar ga manema labarai, yace Tinubu ne yake da tsarika tare da tanadi masu yawa duk don matasan Najeriya da son ganin cigabansu
  • Ya tuna lokacin da Tinubu yake Gwamnan Legas, yace matasa ne suka fi kowa morar romon damokaradiyya saboda ya tallafa musu da sana’o’in dogaro da kai

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Enugu ta gabas, Chimaroke Nnamani, ya bukaci matasa a fadin kasar nan da su zabi ‘dan takarar shugabancin masa na APC, Bola Ahmed Tinubu, inda yace yana da tsarika masu kyau ga matasa.

Bola Ahmed Tinubu
Angulu da Kan Zabo: Sanatan PDP Yana Rokon Matasa da Su Zabi Tinubu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Nnamani, Sanata karkashin jam’iyyar PDP, yace tsohon gwamnan jihar Legas din ya nuna cewa yana duk wasu shiri da suka dace da matasa.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya Su Shiryawa Takarar Kirista-Kirista, Babu Musulmi Inji Mai dakin Tinubu

Sanatan a wata takarda da ya fitarwa manema labarai a Abuja ranar Alhamis, yace a yayin da Tinubu ya hau mulki a 1999, ya dinga fitar da tsarika irin su shawo kan rashin aikin yi, kawo daidaito kan manyan kalubalen da suka addabi matasa a 1999.

Yace Legas a wancan lokacin ta fuskanci hijirar matasa duk don neman aiki bayan da Tinubu ya gane cewa babban ibtila’in barin matasa babu lura kuma hakan yasa ya kaddamar da guguwar canji da suka farfado da tattalin arziki tare da tabbatar da cewa ta hada da yawancin jama’a wadanda matasa ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, kamar yadda yace, ‘dan takarar shugabancin kasan ya samar da gangamin yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi domin wayarwa da matasa kai game da illolin miyagun kwayoyi wadanda ke tarwatsa matasa.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne

“Domin kara shawo kan lamarin, Tinubu ya raba sama da miliyan daya na tallafi ga kowacce kungiyar wayar da kai ta matasa saboda kokarin da suke yi wurin wayar da kai tare da kara musu karfin guiwa.
“Tinubu ya kara yawan kudin ciyarwa na gidajen gyaran hali ta yadda mazauna gidajen zasu nemi ilimi tare da nishadi da zai musu amfani.
“Gwamnatin Tinubu ta kawo cigaba a wuraren koyar da sana’o’i a watan Maris din 2003 domin gyara halayyar ‘yan daba, yaran unguwa da kuma wadanda ke gararamba da suke son gyara rayuwarsu. An koya musu sana’o’i irinsu kafintanci, hada takalma, gyaran kai da rini.”

- Sanatan yace.

Nnamani Gwamnan jihar Enugu ne tsakanin 1999 zuwa 2007 lokacin da Tinubu yake shugabancin jihar Legas.

Sanatan PDP ya samu shiga tawagar neman zaben Tinubu

A wani labari na daban, Sanata Chimaroke Nnamani na jam’iyyar PDP ya samu shiga tawagar gangamin yakin neman zaben Tinubu.

Sanatan mai wakiltar mazabar Enugu ta gabas ya shiga wannan jerin sunayen amma Farfesa Yemi Osinbajo bai samu shiga ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel