2023: Abinda Yasa Ban Sanya Hoton Atiku a Motocin Kamfe Ba, Gwamnan PDP

2023: Abinda Yasa Ban Sanya Hoton Atiku a Motocin Kamfe Ba, Gwamnan PDP

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya fayyace gaskiyar dalilin rashin ganin Hoton Atiku a Motocin kamfe ɗinsa
  • Makinde na cikin tawagar G5 da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ke jagoranta, waɗanda ke takun saka da shugabancin PDP
  • A bayanansa, Gwamnan yace har yanzun ana ci gaba kokarin neman hanyar warware rigingimun cikin gida a PDP

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kare rashin ganin hoton ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, a jikin Motocin Kamfen na jiharsa, yace ba dole bane.

Leadership ta rahoto cewa Gwamnan wanda ya yi jawabi a Ibadan, yace ba laifi bane don ɗan siyasa ya zabi kalar dabarun yakin neman zaɓen da yake so.

Gwamna Seyi Makinde.
2023: Abinda Yasa Ban Sanya Hoton Atiku a Motocin Kamfe Ba, Gwamnan PDP Hoto: Seyi Makinde
Asali: UGC

Yayin da aka tambaye shi ko meyasa aka nemi hoton Atiku aka rasa a jikin Motocin kamfen da aka tsara a gidansa dake yankin Ikolaba, Ibadan, Makinde ya ce:

"A gidana ne kaɗai kuka ga irin waɗannan motocin da aka yi wa zanen Kamfe? Ni na ga wasu Motocin kamfen yan takarar majalisar jiha, sun sa hoton yan takarar majalisar wakilai na yankunansu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk wanda ya sa kudinsa aka tsara masa mota don kamfe, ba zaka tilasta masa ya sa Hotona ko hoton wani ba domin a zaɓe shi.

Wane mataki ake a kokarin sulhun PDP?

Gwamna Makinde ya bayyana cewa fusatattun gwamnon PDP waɗanda aka fi sani da G5 sun gabatar da bukatunsu a kokarin sulhun da ake ci gaba da yi a jam'iyyar PDP.

Mambobin G5 sun haɗa da, Nyesom Wike (Ribas), Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benuwai), Ifeanyi Ugwanyi (Enugu) da Okezie Ikpeazu (Abiya) sun shata layi, sun bukaci Ayu ya yi murabus.

"Na san cewa duk waɗanda suka sauya sheka, sun yanke hakan ne domin cika burinsu na siyasa. Ana ci gaba da kokarin lalubo bakin zaren domin haɗa kan mambobi gabanin zaben 2023."

- Gwamna Makinde.

Dan Takarar Gwamna a Jam'iyyar LP Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

A wani labarin kuma Babban Jigon Jam'iyyar LP kuma tsohon ɗan takarar gwamna a Osun ya sauya sheka zuwa PDP

Yayin gangamin yakin neman zaɓen shugaban kasa na PDP a Osun, Gwamna Adeleke ya sanar da sauya shekar Yusuf Lasun zuwa inuwar laima.

Manyan jiga-jigan PDP da suka haɗa da Atiku Abubakar, Gwamna Okowa, Gwamna Udom Emmanuel duk sun halarci gangamin a Osogbo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel