2023: Dan Takarar Gwamna a Jam'iyyar LP Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

2023: Dan Takarar Gwamna a Jam'iyyar LP Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Osun a inuwar LP, Yusuf Lasun, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ranar Laraba
  • Gwamna Ademola Adeleke ne ya sanar da samun wannan ci gaban a wurin gangamin yakin neman zaben shugaban ƙasa a Osogbo
  • Atiku Abubakar, Iyorchia Ayu, gwamna Okowa, gwamna Udom Emmanuel na cikin jiga-jigan PDP da suka halarci taron

Osun - Ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party a zaɓen gwamnan jihar Osun 2022, Lasun Yusuf, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Gwamnan jihar, Ademola Adeleke ne ya sanar da sauya sheƙar ɗan siyasan a wurin gangamin yakin neman zaɓen shugaban kasa da ya gudana ranar Laraba a Osogbo.

Lasun Yusuf.
2023: Dan Takarar Gwamna a Jam'iyyar LP Ya Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: leadership
Asali: Twitter

Gangamin ya samu halartar ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da abokin takararsa kuma gwamnan jihar Delta, Ufeanyo Okowa.

Kara karanta wannan

Ta Faru Ta Kare, Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Tinubu a 2023

Channels tv ta tattaro cewa shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, shugaban kwamitin kamfen shugaban kasa kuma gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel da sauran ƙusoshi sun halarci wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yusuf Lasun ya rike kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya kuma ya fafata da Adeleke a zaɓen gwamnan jihar Osun da ya gabata ranar 16 ga watan Yuli, 2022, amma ya sha ƙasa.

Jam'iyyar PDP ta samu wannan ci gaban ne duk da rigingimun dake faruwa a cikin gida musamman abinda ya shafi tsagin gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Wike tare da 'yan tawagarsa da ake kira G5 mai ƙunshe da gwamnoni 5 da wasu kusoshin siyasa sun shata layi ne da shugabancin jam'iyyar PDP.

Fusatattun mambobin sun ce ya zama wajibi a yi adalci, shugaban PDP na ƙasa ya sauka ya ba ɗan kudu tun da ɗan arewa ne ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Cikar Kwari Yayin Da Masari Ya Mika Tuta Ga Ɗan Takarar Gwamnan Katsina a 2023

Yakubu Dogara ya koma PDP daga APC

A wani labarin kuma Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP

Dogara ya ɗauki wannan matakin ne awanni bayan shi da wasu jiga-jigan arewa sun aje tafiyar Bola Tinubu, sun rungumi Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Mambobin APC kiristoci a arewacin Najeriya sun jima suna yaki da uwar jam'iyya kan tsayar da mabiya addini ɗaya a matakin takarar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel