Ana Shirin Tarban Dan Takarar Shugaban Kasa, Dan Takarar Majalisa Ya Mutu a Imo

Ana Shirin Tarban Dan Takarar Shugaban Kasa, Dan Takarar Majalisa Ya Mutu a Imo

  • Ɗan takarar majalisar dokokin jihar Imo karkashin inuwar jam'iyyar LP, Chukwunonye Irouno, ya riga mu gidan gaskiya
  • Wani makusancinsa yace rasuwarsa ta tada hankali domin ya shiga gida kenan ya nemi a kawo masa abinci rai ya yi halinsa
  • Kafin mutuwarsa, marigayin ya kasance babban hadimin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha

Imo - Ɗan takarar mamban majalisar dokokin jihar Imo mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Erigwe karkashin inuwar Labour Party, Chukwunonye Irouno, ya kwanta dama.

Irouno, babban mai taimakawa tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, kan harkokin hulɗa da jama'a da nishadi, ya mutu ne a gidansa da ke Owerri, ranar Litinin.

Tutar jam'iyyar LP.
Ana Shirin Tarban Dan Takarar Shugaban Kasa, Dan Takarar Majalisa Ya Mutu a Imo Hoto: punchng

Marigayin, wanda aka tsara zai yi aikin mai gabatarwa a wurin gangamin Peter Obi, ya rasu ne jim kaɗan bayan shi da wasu jiga-jigan LP sun gama duba filin wasan Kanu Nwankwo dake Owerri.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sun duba filin ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da gangamin yakin neman zaɓen Obi a jihar Imo ranar Talata 6 ga watan Disamba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani abokin marigayin ya shaida wa manema labarai cewa ɗan takaran yace ga garinku nan mintuna kaɗan bayan ya koma gidansa na Owerri.

Yace, "Irouno ya rasu, ya dawo gidansa kenan ya umarci matarsa ta kawo masa abinci, ya shiga daki domin ya shirya. Yana zama kan gado sai ya fara wasu sabbin abubuwan kamar barkwanci."

"Ya'yansa suka rasa gane kansa, nan da nanm suka ruga kirawo mamarsu a ɗakin girki, kafin ta ƙariso rai ya yi halinsa."
"Abun kamar almara, shi ne mutumin da ya dace ya jagoranci al'amuran gangamin kamfen shugaban ƙasa na LP a Owerri. Ya mutu mintuna kaɗan bayan ya nemi matarsa ta kawo masa abinci."

Dan Takarar Majalisar Tarayya a Jihar Oyo Ya Kwanta Dama

A wani labarin kuma Dan Takarar Majalisar Tarayya Ya Kwanta Dama Bayan Halartar Taro a Jihar Oyo

Allah ya yi wa Ɗan takarar mamban majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Atisbo/ Saki East/Saki West, jihar Oyo a inuwar inuwar Accord Party rasuwa.

An ce marigayin ya halarci taro a Saki daga baya ya fara zancen ba ya jin daɗi, nan take aka maida sho gidansa dake Jihar Legas, inda rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel