Gwamna Yahaya Bello Ya Ziyarci Nyesom Wika Na Ribas, Sun Sa Labule

Gwamna Yahaya Bello Ya Ziyarci Nyesom Wika Na Ribas, Sun Sa Labule

  • Kodinetan Matasa na PCC-APC, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ziyarci takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike
  • Wannan ziyara ta gwamna Bello na jam'iyyar APC ita ce ta baya-baya da wani jigon siyasa ya kaiwa Wike har gida a Patakwal
  • Wike, jagoran G5 ya kafa sharaɗin canza shugabancin PDP ta ƙasa kafin ya tallata ɗan takara, Atiku Abubakar

Rivers - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kai ziyara ga takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, a gidansa na kai da kai dake Patakwal, babban birnin jihar ranar Jumu'a da daddare.

Bello, gwamna na jam'iyyar All Progressive Congress watau APC, ya kasance jigon siyasa na baya-bayan nan da ya lallaɓa zuwa gidan Wike na Rumuepriokom suka sa labule.

Yahaya Bello tare Wike.
Gwamna Yahaya Bello Ya Ziyarci Nyesom Wika Na Ribas, Sun Sa Labule Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ba'a bayyana ainihin manufa da kuma batutuwan da gwamnomin biyu suka tattauna ba bayan taron ya karkare a sirrance.

Kara karanta wannan

2023: Tashin hankali ga PDP, dangin abokin takararsa sun koma APC, tsagin Tinubu

Gwamna Bello, shi ne Ko'odinetan matasa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a APC yayin da Gwamna Wike ya zare kansa daga tawagar kamfen Atiku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike, shugaban tawagar G5 waɗanda ake kira da 'Tawagar gaskiya' ya shata layi a jam'iyyar PDP ya ce ba zai tallata ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ba, har sai Iyorchia Ayu ya yi murbaus.

Yayin kaddamar da Titin da gwamnatinsa ta gida a makon nan da ya ƙare, Wike ya roki mutanen Ribas su zabi jam'iyyar PDP a zabukan gwamna, majalisun tarayya da na jiha.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa game da ɗan takarar shugaban kasa kuwa, Wike ya bukaci al'ummar Ribas su saurare shi, nan ba da jimawa zai faɗa musu wanda zasu ba kuri'unsu a 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Magoya Bayan Atiku A Ribas Sun Aike Wa Wike Sako Mai Ƙarfi

Ana hasashen dai rigingimun dake wakana a cikin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ka iya ja wa ɗan takararta rashin nasara matukar ba'a warware matsalar ba gabanin 2023.

Jam'iyyar APC ta samu ƙarin goyon baya a Nasarawa

A wani labarin kuma Dubbannin mambobin jam'iyyun PDP da LP sun sauya sheka zuwa APC a Jihar Nasarawa

Yayin gangamin yakin neman zaɓe a ƙaramar hukumar Nasarawa, Gwamna Abdullahi Sule ya yi maraba da masu sauya shekar akalla mutane 2,000.

An tattaro cewa masu sauya sheƙar daga yankin ƙaramar hukumar Nasarawa sun ƙunshi mambobin jam'iyyu biyu na sahun gaba PDP da LP kuma yan ƙabilar Bassa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel