Mambobin Jam'iyyar PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Nasarawa

Mambobin Jam'iyyar PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Nasarawa

  • Mambobin jam'iyyun PDP da Labour Party sama da 2,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki APC a jihar Nasarawa
  • Gwamna Abdullahi Sule, wanda ya tarbe su a wurin gangami ranar Asabar, ya basu tabbacin sun zo gida, ɗaya suke da kowa
  • Ana hasashen fafatawa zata fi zafi a tsakanin manyan jam'iyyu uku watau APC, PDP da LP a babban zaɓen 2023

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya karɓi mutane sama da 2,000 'yan ƙabilar Bassa, waɗanda suka ayyana goyon bayansu ga jam'iyyar APC.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mutanen sun ƙunshi mambobin jam'iyyar PDP da Labour Party kuma sun tabbatar da mubaya'arsu ga APC ne yayin ralin kamfe da ya gudana a ƙaramar hukumar Nasarawa.

Tambarin jam'iyyar APC.
Mambobin Jam'iyyar PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Nasarawa Hoto: punchng
Asali: UGC

Da yake maraba da masu sauya sheka zuwa inuwar APC, gwamna Sule yace daga yanzu sun zama ɗaya da kowane mamba, ba za'a nuna musu banbanci ba.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Gwamnan ya jaddada kwarin guiwarsa cewa bisa la'akari da yawan mutanen da suka fito wannan gangami, mazauna yankin sun nuna shirinsu na goyon bayan APC a 2023 kamar yadda suka yi a zaɓukan baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"A dunkule muke a APC, muna ganin yadda wasu ke barin jam'iyyunsu suna zuwa su haɗa kai da mu saboda suna ganin yadda muka haɗa kanmu. Duk mamba mai biyayya ba zai so ta da yamutsi a jam'iyyarsa ba."

A nasa jawabin, shugaban kwamitin kamfen APC na jihar, Sanata Abubakar Sodangi ya roki masu ruwa da tsakin APC a yankin da su ɓinne saɓanin dake tsakaninsu domin nasarar jam'iyya a zaɓe mai zuwa.

A kalamansa yace:

"Ya zama dole dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kansu kuma su yi aiki tare don jam'iyyar APC ta kai ga nasara, muna buƙatar haɗa karfi da karfe mu tabbata APC ta kai labari a ƙaramar hukumar Nasarawa."

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Hargitse a Jihar Arewa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

"Naji daɗi matasa da mata na tare da mu wajen aiki ba dare ba rana da nufin tabbatar da baki ɗaya 'yan takarar APC sun ci zaɓe."

Mun Tafka Babban Kuskure a Rikicin PDP, Shugaban Kwamitin Kamfen Atiku

A wani labarin kuma shugaban kwamitin yakin neman zaɓen PDP na ƙasa yace Atiku da sauran kusoshin jam'iyya sun tafka babban kuskure

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel yace duk da haka yana da yaƙinin za'a lalubo mafita don gyara kuskuren gabanin 2023.

Da yake bayyana kwarin guiwar kawo karshen taƙaddamar cikin gida a PDP, gwamnan yace kowace kuri'a ɗaya tana da muhimmanci idan har jam'iyyar na fatan lashe zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel