Tashin hankali ga su Atiku, jiga-jigan jihar mataimakinsa sun kama tafiyar Tinubu

Tashin hankali ga su Atiku, jiga-jigan jihar mataimakinsa sun kama tafiyar Tinubu

  • Wasu masu fada a ji kuma na kusa da gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta sun saki PDP, sun kama hanyar su Bola Tinubu a APC
  • Wadannan jiga-jigai dan sun fito ne daga unguwanni daban-daban ciki har hada da Owa-Alero 2, rumfar zaben Okowa
  • Gwamnan na Delta da ke kan wa'adinsa na karshe shine abokin takarar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP

Jihar Delta - Daruruwan magoya bayan jam'iyyar PDP daga karamar hukumar su gwmana Ifeanyi Okowa, Ika ta Arewa ne suka bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Tsoffin magoya bayan na PDP yayin barin jam'iyyar sun bayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmad Tinubu a takararsa ta shugaban kasa a APC.

Hakazalika, sun ce Ovie Omo-Agege za su zaba a matsayin gwamnan jihar, kamar yadda rahoton Vanguard ta bayyana.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Magoya Bayan Atiku A Ribas Sun Aike Wa Wike Sako Mai Ƙarfi

Sun bayyana cewa, duk da suna da gwamna dan yankinsu, ayyukan da aka yi musu an yi su ne ta dalilin gwamnatin APC karkashin jagorancin Buhari.

An ruwaito cewa, sanata Ovie Omo-Agege, shugaban APC na Delta Omeni Sabotie da Hon, Friday Osanebi ne suka karbe su zuwa jam'iyyar a yayin wani gangamin kamfen a jihar.

An kuma tattaro cewa, jama'ar sun fito ne daga unguwanni daban-daban, ciki har da rumfar zaben gwamna Okowa, Owa-Alero.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mambobin PDP sun sauya sheka, sun koma APC a jihar Delta
Tashin hankali ga su Atiku, jiga-jigan jihar mataimakinsa sun kama tafiyar Tinubu | Hoto: @OvieOmoAgege
Asali: UGC

Tun farko dama dan takarar gwamnan APC a jihar ya ce, kada 'yan jihar su amince da ci gaba da mulkin Okowa ta hanyar kakaba musu dan takara, rahoton This Day.

Kofa a bude take ga duk son shiga APC, inji shugabanta a Delta

Yayin da yake karbarsu, shugaban APC na jihar ya ce, kofa a bude take ga duk wani dan Delta da ke son shiga jam'iyyar APC, musamman wadanda suka damu da abin da Okowa ya yi cikin shekaru bakwai.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Tinubu zai tafi jihar su wani tsohon shugaban kasa na PDP yin kamfen ranar Alhamis

Ya kuma kara da cewa, babu shakka tsoffin mambobin na PDP sun gaji da mulkin gwamna Okowa na tsawon shekaru.

A bangare guda, ya yabawa Hon Chamberlain Dunkwu, hadimin kakakin majalisar wakilai ta kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila bisa jawo mambobin PDP zuwa APC da kuma kawo manyan ayyuka a karamar hukumar Iko ta Arewa.

A bangare guda, Omo-Agege ya ce zai yi tafiya da Yahoo Boys wajen habaka tattalin arziki da kuma sauya aikinsu na barna ya dawo na kirki idan ya zama gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel