Matar Atiku Abubakar Ta Shawarci Yarbawa Kan Dan Takarar Shugaban Kasan da Ya Dace Su Zaba a 2023

Matar Atiku Abubakar Ta Shawarci Yarbawa Kan Dan Takarar Shugaban Kasan da Ya Dace Su Zaba a 2023

  • Titi Atiku ta ce za a samu bayarabiya ta farko a matsayin matar shugaban kasar Najeriya idan har mijinta ya dare kujerar mulki a 2023
  • Matar Atiku Abubakar ta yi ikirarin cewa zaban dan takarar shugaban kasar na PDP kamar zaban bayarabe ne saboda ita
  • Ta yi alkawarin cewa mijinta zai kawo karshen yan ta'addan Boko Haram idan har ya dare kujerar Buhari domin shi Bafilatani ne amma ba makashi ba

Ondo - Titi Abubakar, uwargidar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ta bukaci yan kudu maso yamma da su zabi mijinta a matsayin shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A cewarta, zaban Atiku daidai yake da zaban Bayarabe domin itama yar cikinsu ce, Jaridar Independent ta rahoto.

Titi da Atiku
Matar Atiku Abubakar Ta Shawarci Yarbawa Kan Dan Takarar Shugaban Kasan da Ya Dace Su Zaba a 2023 Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, 39 ga watan Nuwamba a wajen gangamin jam’iyyar a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Titi ta kuma bukaci mazauna jihar da kada su yarda jam’iyyar adawa ta All Progressive Congress (APC) ta yaudare su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mijina zai murkushe Boko Haram idan ya lashe zabe a 2023, Titi Atiku

Nigerian Tribune ta rahoto cewa uwargidar Atiku ta kuma yi alkawarin cewa mijinta zai murkushe Boko Haram da daukar nauyin karatun dalibai.

Titi ta ce:

“Mutane na, gani tsaye a gabanku don fada maku cewa mijina yayi kokari a baya. Mijina ne ya lashe zaben karshe da aka yi amma aka yi mana fashi. Tabbass mijina Bafulatani ne amma shi ba makashi bane kuma mun dade tare. Na koyar da shi al’adunmu, kuma shi din dan cikinmu ne.
“Atiku zai murkushe Boko Haram kuma zai dauki nauyin karatunku kyauta.
“Babu Bayarabiyar da ta taba rike mukamin matar shugaban kasa kuma idan muka zabi Atiku, kuri’ar Yarbawa ce. Akwai yunwa a kasar, kada ku yarda masu adawa su yaudare ku, ku zabi dukkanin yan takarar PDP a yayin zaben.”

Aisha Buhari ta shawarci yan siyasar arewa da su yi koyi da ba kudu

A wani labarin, Hajiya Aisha Buhari, uwargidar shugaban kasar Najeriya ta bukaci yan siyasa a arewa da su yi koyi da takwarorinsu na yankin kudu domin samun ci gaban da ake bukata.

Aisha Buhari ya nemi a dunga baiwa mata damar shiga a dama da su a harkokin shugabanci musamman ma a matsayin mataimakan gwamnoni a jihohin arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel