Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

  • Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya ce babu wanda ya fi dacewa ya mulki a Najeriya a 2023 fiye da Bola Tinubu
  • Tsohon kakakin majalisar dokoki na tarayyar ya ce mutum ne mara nuna kabilanci ko tsatsauran ra'ayin addini kuma gogagge a bangarorin mulki, gina al'umma da sauransu
  • Masari ya kuma ce yana kyautata zaton jam'iyyar APC za ta ci zaben gwamna a Katsina saboda ayyukan da gwamnatinsa ta yi a shekaru 8 da suka gabata da cancantar dan takarar da jam'iyyar ta tsayar

Katsina - Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu ne zabi mafi cancanta ga Najeriya a 2023.

Ya ce Tinubu ya dara sauran yan takarar shugaban kasar a bangarorin kafa tarihi, asali da ayyukan cigaba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Surukin Shugaba Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC, Ya Fadi Dalili

Bola Tinubu
Masari: Tinubu Ne Zabi Mafi Cancanta Ga Yan Najeriya A 2023. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Masari ya furta hakan ne yayin wani hira ta musamman da ya yi da The Nation a ofishinsa da ke Katsina.

Ya bayyana Tinubu a matsayin wani abu mai daraja a kasar nan kuma zai cigaba da amfanar Najeriya idan aka zabe shi shugaban kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Masari:

"Tarihin Tinubu lokacin da ya ke ofis ya nuna ya dauki mutane daga kabilu daban-daban aiki, kuma tsohon sanata ne, mai bada tallafi, mai goyon bayan dimokradiyya kuma ana iya ganin wadanda suka amfana da shi.
"Ba a san shi da nuna kiyayya ba ko fifiko da kabilanci ko tsatsauran ra'ayin addini yayin da yana da wahala a gano abubuwan cigaban da abokan hamayyarsa suka yi baya ga yawon bude ido da biyewa yan kazangi."

Dalilin da yasa APC za ta ci zaben gwamna a Katsina - Masari

Kara karanta wannan

2023: Ya zama wajibi dukkan Musulmi ya zabi Tinubu, inji wata kungiyar Musulmai

A cewar rahoton na The Nation, Masari ya yi kira ga yan Najeriya su sani cewa zaben Tinubu a shekarar 2023 abu ne da ya zama dole saboda tsayayyiyar kasa da cigaba.

Game da yiwuwar nasarar APC a jihar Katsina, gwamnan ya ce cigaban da gwamnatinsa ta samu a shekaru takwas da suka gabata da cancantar dan takarar jam'iyyar zai tabbatar da samun nasarar jam'iyyar.

Zaben 2023: Sauran kiris in zama shugaban kasa, In Ji Tinubu

Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ya ce saura matakai kadan ya zama shugaban kasa na gaba a Nigeria.

A cewar rahoton Vanguard, Tinubu ya furta hakan ne yayin tattaunawa da shugabannin darikar Tijaniyya a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel