Aisha Buhari: Abunda Ya Kamata Yan Siyasar Arewa Su Koya Daga Takwarorinsu Na Kudu Maso Yamma

Aisha Buhari: Abunda Ya Kamata Yan Siyasar Arewa Su Koya Daga Takwarorinsu Na Kudu Maso Yamma

  • Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta magantu a kan rikicin APC reshen jihar Adamawa
  • Aisha Buhari ta shawarci yan siyasar arewa da su yi koyi da na kudu wajen nada mata a mukamai musamman kujerar mataimakan gwamna
  • Ta kuma jinjinawa shugabannin jam'iyyar mai mulki kan yadda suka shiga lamarin siyasa a mahaifarta

Uwargidar shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga shugabannin Arewa da su yi koyi da takwarorinsu na kudu maso yamma wajen nada mata a matsayin mataimakan gwamna.

Aisha ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Adamawa.

Aisha Buhari
Aisha Buhari: Abunda Ya Kamata Yan Siyasar Arewa Su Koya Daga Takwarorinsu Na Kudu Maso Yamma Hoto: aishambuhari
Asali: Instagram

Masomin rikicin APC a jihar Adamawa

Daily Trust ta rahoto cewa rikici ya barke a jihar bayan Sanata Aishatu Binani ta lashe zaben fidda dan takarar gwamna a jihar, inda daya daga cikin yan takarar, Malam Nuhu Ribadu ya yi watsi da hakan sannan ya garzaya kotu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A watan da ya gabata, babbar kotun tarayya ta soke zaben fidda gwanin sannan ta ayyana cewa jam’iyyar bata da dan takarar gwamna a jihar, lamarin da yasa APC da Binani tunkarar kotun daukaka kara kan hukuncin.

Tuni shari’ar ta raba kan mambobin jam’iyyar tsakanin masu goyon bayan Binani da magoya bayan Ribadu.

Sai dai kuma, a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, kotun daukaka kara mai zama a Yola, babban birnin jihar Adamawa ta ayyana Binani a matsayin yar takarar gwamnan jihar na APC.

Matsayina a kan siyasar Adamawa, Aisha Buhari

Da take martani kan lamarin a Instagram, uwargidar shugaban kasar ta ce:

“Ina mai farawa da suna Allah, ina mai mika godiyata ga shugabannin APC reshen jihar Adamawa kan ziyarar ban girma da suka kawo mun a ranar 18 ga watan Nuwamban 2022.

“A matsayina na yar jihar, uwa, kaka kuma uwargidar shugaban kasar Najeriya, zan so sake jadadda goyon bayana ga damuwar shugabannin jam’iyyarmu, tare da yunkurin shuga matsalar don tunani da hankali su shiga cikin siyasar Adamawa.
“Zan sake nanata rokona ga shugabanni a arewa da su koyi darasi daga ayyukan takwarorinsu na kudu maso yamma wajen nada mata a matsayin mataimakan gwamna a jihohi a kokarin shigar da jinsi a siyasarmu.
“Wannan shine mataki na gaske a kokarinmu na cimma manufar aldalci a tsakanin jinsi maimakon ra’ayin gashin kai mara amfani na dan siyasar a mutu ko ayi rai.”

Aisha Binani ta dawo mahaifarta bayan nasara kan Ribadu a kotun daukaka kara

Mun ji a baya cewa Aisha Binani, yar takarar gwamna na jam'iyyar APC a Adamawa ta samu tarba ta musamman daga masoyanta yayin da ta dira a mahaifarta da ke garin Yola.

Kotun daukaka kara ce ta dawo da Binani kan kujerarta na yar takarar gwamna a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel