Kangin Talauci: Yan Najeriya Za Su Ba APC Karin Dama – Jigon APC

Kangin Talauci: Yan Najeriya Za Su Ba APC Karin Dama – Jigon APC

  • Jigon jam'iyyar APC, Bala Ibrahim, ya yi ikirarin cewa ba a taba gwamnatin da ta yaki talauci a Najeriya kamar ta Buhari ba
  • Kakakin APCn wanda ya nuna tabbacin yan Najeriya za su sake zabar su a 2023 ya ce mutane da yawa sun zama attajirai a gwamnatin
  • Ibrahim ya kuma ce PDP ce ta jefa mutum miliyan 133 da NBS ta ce suna fama da talauci sabod mulkin kama karya da ta shafe shekaru 16 tana yi

Daraktan labarai na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bala Ibrahim, ya bayyana dalilan da zai sa yan Najeriya su sake ba jam’iyyar mai mulki wata dama a babban zaben 2023.

Ibrahim ya bayyana cewa babu wata gwamnati da ta yi kokari wajen yakar talauci a tarihin Najeriya kamar gwamnatin da APC ke jagoranta, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Buhari
Kangin Talauci: Yan Najeriya Za Su Ba APC Karin Dama – Jigon APC Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

PDP ce ta jefa mutane cikin talauci saboda shekaru 16 da ta shafe kan mulki

Da yake martani ga rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) kan cewa yan Najeriya miliyan 133 na cikin kangin talauci, Ibrahim ya ce gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da wasu yan Najeriya miloniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels, Ibrahim ya ce:

“Ina farin ciki cewa hukumar NBS bata ce APC bace ta talautar da yan Najeriya. Wannan yalauci da ya mamaye Najeriya ya kasance ne sakamakon mulkin kama karya na PDP tsawon shekaru 16. Tunda ta hau karagar mulki, APC na ta yin duk mai yiwuwa don inganta rayuwar al’umma.
“Ba abu bane da za a iya yi a dare daya, amma idan za ka dauki kididdigan mutanen da aka kai zuwa mataki na gaba, yawan mutanen da aka fitar daga kangin talauci, yawan mutanen da ke farin ciki, musamman mutanen da suka zama miloniya a harkar noman shinkafa, za ka ga cewa babu gwamnati da ta yi kokari sosai wajen yakar talauci a tarihin Najeriya kamar wannan gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

“Wannan ita ce gwamnatin da ta isa ga mutane ta hanyar magana a duk inda suke. Bana tunani wata gwamnati ta taba yin abun da APC ta yi a cikin wannan lokacin, kuma kasancewar sun ga abun da APC ta yi, na yarda yan Najeriya za su sake bata karin dama don yin abubuwa saboda ba za su so komawa ga abun da ya faru a baya ba.”

Legit.ng ta tuntubi wani dan APC mai suna Mallam Ahmad don jin ta bakinsa kan wannan batu inda ya ce lallai gwamnatinsu tayi kokari da mutanenta don shi kansa ya san wadanda suka ci gajiya tallafin kudade kyauta.

Mallam Ahmad ya ce:

“Ni mamban PDP ne a karamar hukumar Ɗanja, jihar Katsina.
“A zahirin gaskiya gwamnatin shugaba Buhari ta maida mutane miliyoniya amma abun tambaya suwa? Mafi yawan waɗanda suka ci gajiyar gwamnatin Buhari su ne masu uban gida, kana da wani a cikin gwamnati ko ƙusa a APC to idan har zai taimakeka nan da nan zaka ɗaga.

Kara karanta wannan

APC ta yi magana, ta ce ba Buhari ya talauta 'yan Najeriya miliyan 133 ba, ta fadi su waye

“Amma idan kai Talaka ne baka da kowa to fa sai dai karin talauci saboda tashin farashi wanda mutane basu tsammani ba.
“ Sai wannan gwamnatin maganar gaskiya ta zo da tsarika masu kyau na taimakawa talakawa tabbas bana kokanto kan haka don ni shaida ne, matsalarta biyu rashin tsaro da tsadar rayuwa.
“Nasan mutanen da suka samu tallafi daga 50,000 zuwa miliyan 1 kyauta don su ja jari amma matsalar mutanen ne babu tsarin kafa kasuwanci a ransu, na san wanda bai san kowa ba ya shiga tsarin FG mai gwabi da sauransu.
“ Akwai abubuwa da dama da aka bullo da su wanda da ace duk wanda Allah ya sa ya samu, ya yi abinda ya dace wlh da yawa yanzun sun zama miliyoniya sosai. Allah ya sa mudace.”

PRP bata hade da APC ba a Sokoto, Sakataren jam'iyyar PRP

A wani labarin kuma, jam'iyyar PRP a jihar Sokoto ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa ta rushe a cikin jam'iyyar APC mai mulki gabannin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: PDP ta fadi irin tanadin da ta yiwa 'yan Najeriya idan Atiku ya ci zabe badi

Babban sakataren PRP na kasa, Malam Ibrahim Tudun-Doki, ya ce wannan ikirarin duk kanzon kurege ne da yaudara cewa suna nan da kafafunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel