Jam'iyyar APC Ta Zargi PDP da Talauta ’Yan Najeriya Miliyan 133

Jam'iyyar APC Ta Zargi PDP da Talauta ’Yan Najeriya Miliyan 133

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai ba APC ce ta jefa 'yan Najeriya cikin bakin talauci da suke ciki ba
  • Jam'iyyar mai ci ta kuma bayyana cewa, jam'iyyar PDP ce ta jefa 'yan Najeriya miliyan 133 cikin bakin talauci cikin shekaru 16
  • An fitar da rahoton da ke nuna adadin talakawan Najeriya, da kuma yankin da ya fi yawan matalauta a Najeriya

Najeriya - Jam'iyyar APC mai mulki ta nesanta mulkin shugaba Muhammadu Buhari da talauta 'yan Najeriya akalla miliyan 133.

Wannan magana na zuwa ne ta bakin daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim yayin da ya bayyana a shirin Sunsise Daily da gidan talabijin na Channels ta gabatar a ranar Litinin.

Yayin da ya ce bai zai musanta binciken hukumar kididdiga ta kasa ba, Ibrahim ya yi ishara da cewa, talaucin da 'yan Najeriya ba komai bane face sakamakon bakin mulkin irin na PDP.

Kara karanta wannan

2023: PDP ta fadi irin tanadin da ta yiwa 'yan Najeriya idan Atiku ya ci zabe badi

A watan Nuwamba ne NBS ta fitar da wani rahoton da ke cewa, akalla akwai 'yan Najeriya miliyan 133 da ke fama da bakin talauci, wanda ke nuna kaso 63% na 'yan kasar matalauta ne.

Hakazalika, rahoton ya ce, kashi 65% na talakawan Najeriya daga yankin Arewacin kasar nan suke, yayin da yankin Kudu ke daukar kaso 35%.

Ba Buhari ne ya jefa 'yan Najeriya a talauci ba, inji APC
Jam'iyyar APC Ta Zargi PDP da Talauta ’Yan Najeriya Miliyan 133 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin jam'iyyar APC

Sai dai, jigon na APC ya kare gwamnatin Buhari, inda yace babu ruwan gwamnatin Manjo Buhari idan ana magana game karuwar talakawa a Najeriya, Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

"na farin cikin cewa, NBS bata ce APC ke ta talauta 'yan Najeriya ba. Wannan talauci da ya yiwa Najeriya katutu sakamakon rashin iya shugabanci ne na PDP a tsawon shekaru 16.
"APC, tun da ta karbi mulki take yin ruwa da tsaki don inganta rayuwa, take kai mutane ga ainihin abin da suke bukata, da kuma alkawarinta na taimakawa jama'a, kuma tana hakan."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Za Su Sake Zabar APC Don Ba a Taba Gwamnati Da Ta Fitar Da Mutane Daga Talauci Kamar Ta Buhari Ba, Jigon APC

Da yake ci gaba da bayani, Ibrahim ya yaba da irin kokarin gwamnatin Buhari, wanda yace ta cancanci lambar yabo na musamman ta hanyar mai da manoman shinkafa attajirai daga watan Mayun 2015 zuwa yanzu.

'Yan Najeriya na ci gaba da koka tsadar abinci da kayayyakin gudanar da rayuwa na yau da kullum tun farkon hawan Buhari zuwa yanzu.

Wani jigon APC ya bayyana cewa, yana fatan 'yan Najeriya su sake ba jam'iyyar dama a zaben 2023 domin daurawa daga inda Buhari ya tsaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel