Asari Dokubo: Atiku ‘Safaya Taya’ ne, Ba Tsarar Gogayya Tinubu Bane

Asari Dokubo: Atiku ‘Safaya Taya’ ne, Ba Tsarar Gogayya Tinubu Bane

  • Mujahid Asari Dokubo, shugaban Niger Delta People’s Salvation Force, ya bayyana goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu
  • Dokubo ya kwatanta Atiku Abubakar matsayin ‘safaya taya’ don bai taba rike mikamin siyasa ba sai mataimakin shugaban kasa
  • Yace Bola Tinubu ya shugabancin Legas na tsawon shekaru 8 sannan shi ne ya kasance akalar da ta sauya labarin jihar Legas

Asari Dokubo, shugaban Niger Delta People’s Salvation Force (NDPSF), yace yana goyon baya Bola Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.

Tinubu da Atiku
Asari Dokubo: Atiku ‘Safaya Taya’ ne, Ba Tsarar Gogayya Tinubu Bane. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

A yayin zantawa da Channels TV, Dokubo ya kwatanta Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne matsayin labarin nasara a jihar.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa, Dokubo yace Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa na Labour Party da kuma Rabiu Musa Kwankwaso, ‘dan takarar shugabancin kasa na NNPP ba sa’o’in karawar Tinubu bane.

Ya kwatanta Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP matsayin safaya taya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A zaben shugabancin kasa, ni ina tare da Tinubu saboda na ga abinda Tinubu yayi a Legas da kuma tarihin da ya bari.”

- Dokubo yace.

“Tinubu yayi gwamnan Legas, ya mikawa Fashola. Yanzu ba zamu iya maganar Atiku ba. Atiku bai taba yin mulki na gwamnati ba, safaya taya ne, tsohon mataimakin shugaban kasa ya taba zama.
“Obi na Labour Party gwamna ne na shekaru 8 kamar Tinubu. Kwankwaso na NNPP gwamnan Kano ne na tsawon shekaru 8. Idan muka hada wadannan ukun, mu cire Atiku saboda bai taba samun iko kamarsu ba.
“Tinubu ya bar mulki kuma ya mikawa Fashola. Yanzu zaku iya hada Fashola na Legas da Willie Obiano da Obi ya dauka? Za ku iya gwada wanda ya gaji Kwankwaso?”

- Ya cigaba da cewa, kamar yadda TheCable ta rahoto.

Kiristocin Arewa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Obi

A wata zantawa da aka yi da Babachir Lawal, yayi kira ga Kiristocin jihohin arewaci 19 na kasar nan da su yi watsi da Boka Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a zaben 2023 dake gabatowa.

Yayi kira garesu da su garzaya ranar zabe su kada kuri’unsu ga Peter Obi tare da Yusuf Datti Baba Ahmed.

Babachir Lawal ya sanar da hakan ne duk don fusata da yayi da tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel