Tikitin Musulmi da Musulmi: Jerin Jiga-jigan APC da Basa Goyon Bayan Tinubu a 2023

Tikitin Musulmi da Musulmi: Jerin Jiga-jigan APC da Basa Goyon Bayan Tinubu a 2023

A watan Yulin 2022, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zabi Kashim Shettima, taohin gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.

Wannan hukunci nasa yasa mambobin APC da yan Najeriya musamman kiristoci kokawa.

Sun caccaki tsohon gwamnan na jihar Lagas a kan daukar Musulmi dan uwansa a matsayin abokin takara, cewa wannan hukunci nasa na iya haddasa rikicin addini a kasar.

Masu adawa da takarar Shettima/Tinubu
Tikitin Musulmi da Musulmi: Jerin Jiga-jigan APC da Basa Goyon Bayan Tinubu a 2023 Hoto:@officialABAT, @OnwardNG, @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Yayin da Tinubu ya sha rokon al'ummar kirista da bayyana dalilinsa na daukar Shettima, wasu masu ruwa da tsaki a APC basu gamsu da muhawararsa ba.

Hakan ya yi sanadiyar da wasu suka janye goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasar na APC. Yayin da wasu suka fice zuwa wasu jam'iyyun, wasu na nan a APC amma sun ce ba zasu marawa takarar Tinubu baya ba.

Kara karanta wannan

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga wasu daga cikin manyan jiga-jigan APC da suka janye goyon bayansu ga Tinubu:

1. Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya taka muhimmiyar rawar gani wajen ganin Tinubu ya samu tutar APC. Sai dai kuma, yana adawa da tikitin Musulmi da Musulmi.

A ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, jigon na APC ya sha alwashin zaban dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, koda dai yace zai ci gaba da kasancewa a APC.

2. Yakubu Dogara

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, shima ya nuna adawa da tikitin Musulmi da Musulmi.

Yayin da Dogara da tsohon SGF Lawal suka yi hadaka a matsayinsu na masu adawa da tikitin addini daya, ba a tabbatar da ko tsohon kakakin majalisar na goyon bayan Atiku bane a zaben shugaban kasar na 2023.

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Ƙasa: Jihohin PDP 7 Masu Ƙarfi Da Atiku Zai Iya Shan Kaye A 2023

3. Sanata Ishaku Abbo, Adamawa ta arewa

Jim kadan bayan sanar da Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu, Ishaku Abbo, sanata mai wakiltan Adamawa ta arewa, ya yi murabus daga kungiyar yakin neman zaben na APC.

Sanatan ya bayya a zaban Shettima da Tinubu yayi a matsayin wanda bai dace ba, yana mai cewa shi zai yi adawa da tikitin addini daya.

Abbo ya ce Tinubu ya ki koyi da magabacinsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya zabi Kirista a matsayin abokin takara a 2015.

4. Daniel Bwala

Ba janyewa daga goyon bayan Tinubu kawai Daniel Bwala yayi ba, harda sauya sheka yayi daga APC zuwa PDP.

Nan take aka nada shi a matsayin kakakin kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawar, Atiku Abubakar.

5. Tonye Princewill

Tonye Princewill, taohon dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar Ribas kuma na hannun daman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi watsi da Tinubu da APC saboda tikitin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Ya Kin Kiristoci, Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki a Wata Jahar Kudu

Tonye ya ce ba zai iya kare hukuncin jam'iyyarsa na yin tikitin Musulmi da Musulmi ba duk da kokawar da yan Najeriya da dama suka yi.

6. Keneth Okonkwo

Hakazalika, shahararren jarumin Kannywood, Kenneth Okonkwo, ya yi murabus daga APC bayan ya yi watsi da hukuncin Tinubu. Ya bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi na APC ya lalata siyasar kiristoci a arewa har abada idan aka bari yayi tasiri.

Jarumin na Nollywood ya koma goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel