Kotun Daukaka Kara ta Jaddada Binani Matsayin ‘Yar Takarar Gwamnan Taraba a APC

Kotun Daukaka Kara ta Jaddada Binani Matsayin ‘Yar Takarar Gwamnan Taraba a APC

  • Kotun daukaka kara dake zama a Adamawa ta dawowa da Sanata Aishatu Binani kujerar takarar Gwamnan APC a jihar Adamawa
  • Kotun ta soke hukuncin babbar kotun tarayya dake Yola wacce ta kwace takarar tare da ayyana cewa APC bata da ‘dan takarar Gwamna a jihar
  • A hukuncin farko, Nuhu Ribadu, tsohon shugaba EFCC yayi nasara inda alkali yace dukkan zaben yayi karantsaye ga dokokin zabe saboda aringizon kuri’u da aka yi

Adamawa - Kotun daukaka kara ta dawo da Aishatu Binani matsayin ‘yar takarar kujerar Gwamnan jihar Adamawa karkashin jam’iyyar APC, jaridar TheCable ta rahoto.

Aishatu Binani
Kotun Daukaka Kara ta Jaddada Binani Matsayin ‘Yar Takarar Gwamnan Taraba a APC. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

A watan Oktoba, wata kotun tarayya dake zama a Yola, babban birnin jihar Adamawa ya so zaben fidda gwani na jam’iyyar APC wanda ya samar da Binani matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar a Adamawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Ɗaukaka Kara Ta Maida Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda shari’ar ta kasance

Kotun ta bayyana cewa, jam’iyyar APC bata da ‘dan takara a a jihar a zaben 2023.

Binani sanata da take wakiltar Adamawa ta tsakiya, Nuhu Ribadu, tsohon shugaban Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin Arzikin kasa ta’annati, EFCC da Jibrilla Bindow, tsohon Gwamnan jihar inda ta ci zaben fidda gwani da aka yi ranar 26 ga watan Mayu.

Binani ta samu kuri’u 430 inda ta lallasa Bindow wanda ya samu kuri’u 103 sannan Ribadu ya samu kuri’u 288.

Sakamakon fusata da suka yi da sakamakon zaben, Ribadu ya shigar da kara kotu wacce ta kalubalanci nasarar Binani.

Channels TV ta rahoto cewa, A hukuncinsa, Alkali Abdulaziz Anka ya soke dukkan zaben fidda gwanin.

Ya yanke hukuncin cewa, zaben bai yi biyayya ga dokokin zabe na 2022 ba na kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: FG Ta Kwato $1b Daga Masu Satar Kudin Najeriya Tun Daga 2015

Alkalin yace nasarar Binani kai tsaye ta yi karantsaye ga sashi na 85 na dokokin zabe saboda an saka kuri’u da suka fi masu zaben yawa.

Kotu ta yanke hukunci kan karar Tinubu

A wani labari na daban, babbar kotun tarayya dake zama a Abuja tayi fatali da karar da APP ta shigar domin hana Bola Tinubu takara.

Jam’iyyar APP ce ta tare da wasu ta shigar da karar inda aka ayyana hukumar INEC ce wacce ake kara ta farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel