Daga Karshe Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Ta Nemi a Hana Tinubu Takara a 2023

Daga Karshe Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Ta Nemi a Hana Tinubu Takara a 2023

  • Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta kawo karshen karar neman a soke takarar Bola Tinubu a zaben 2023
  • Da take yanke hukunci ranar Litinin Kotun ta yi watsi da ƙarar sakamakon rashin ɗaukar shari'a da muhimmanci daga bangaren masu ƙara
  • Jam'iyyar Action Peoples Party (APP) tare da wasu ne suka maka INEC, Tinubu da jam'iyyar APC a gaban Kotun

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da wata ƙara da jam'iyyar Action Peoples Party (APP) ta shigar gabanta, tana bukatar a rushe takarar Bola Tinubu na APC.

Daraktan Midiya da Yaɗa labarai na kwamitin kamfen shugaban ƙasa na APC, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Bola Ahmed Tinubu.
Daga Karshe Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Ta Nemi a Hana Tinubu Takara a 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Yace a ƙarar mai lamba FHC/UM/CS/124/2022 jam'iyyar APP da wasu sun ayyana hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a matsayin wanda ake ƙara ta farko.

Kara karanta wannan

Tinubi Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

Haka nan sun sanya ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, da jam'iyyar APC a matsayin waɗanda da ake ƙara na biyu da na uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Masu shigar da ƙara sun roki Kotu ta umarci INEC ta soke takarar Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC. Sun zargi cewa Tinubu ya miƙa wa INEC bayanan ƙarya a Fam EC9."
"Sun ce ya gaza bayyana karatunsa na Firamare da Sakandire kamar dai yadda yake a ƙunshe a Fam CF001 da ya cike a 1999 lokacin da yake neman zama gwamna kuma hakan ya saɓa wa sashi na 29 a kundin dokokin zaɓe 2022."

- Bayo Onanuga.

Ya ƙara da cewa Lauyan APC ya kawo hanzarin cewa tun farko ƙarar ta saba wa doka, inda ya shaida wa Kotun cewa bukatun da masu shigar da ƙarar basu da hurumi.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Manyan 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a Ba Masaka Tsinke a Jiha Ɗaya

Mista Onanuga yace Lauyan ya kuma yi musun cewa ƙarar ba ta da tushe kuma ɓata lokacin shari'a ne kawai.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

"Da aka dawo zaman shari'ar a gaban Mai shari'a Emeka Nwite na babbar Kotun tarayya ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba, 2022, aka nemi masu ƙara aka rasa a harabar Kotu."

"Nan take Alƙalin ya kori ƙarar saboda rashin ɗaukar hukunci da muhimmanci," inji Darakta yaɗa labaran PCC-APC.

A wani labarin kuma Tinubu ya gamu da wata sabuwar matsala, Tsohon SGF a mulkin Buhari, yace yana nan a APC amma ɗan takarar PDP zai wa aiki

Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jigo a APC yace shi da magoya bayansa ba zasu zaɓi Musulmi da Musulmi ba a 2023.

Yace sun cimma yarjejeniya da jam'iyyar PDP kuma duk randa Buhari ya aje siyasa daga ranar shi ma zai barta.

Kara karanta wannan

Magoya Baya da Makusantan Jonathan Sun Yanke Shawara, Sun Faɗi Wanda Suke So Ya Gaji Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel