Gwamnatin Buhari ta Bayyana Adadin Kudin da Ta Kwato Daga Mahandama tun Daga 2015

Gwamnatin Buhari ta Bayyana Adadin Kudin da Ta Kwato Daga Mahandama tun Daga 2015

  • Gwamnatin Buhari ta sanar da cewa ta samo $1 biliyan na kudaden da mahandama suka wawure a kasar nan tun bayan hawan mulkinsa
  • Abubakar Malami, antoni janar na tarayya kuma ministan shari’a na kasar nan ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati a Abuja
  • Ya bayyana cewa, an waskar da kudaden zuwa sassan amfani masu yawa a kasar nan da suka hada da tattalin arziki tare da yaki da fatara

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya tace $1 biliyan ta kwato daga kudaden da aka wawure tun bayan hawan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kudaden da aka samo daga mahandama
Gwamnatin Buhari ta Bayyana Adadin Kudin da Ta Kwato Daga Mahandama tun Daga 2015. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Yayi wannan jawabin ne a yayin zantawarsa da manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwa na tarayya a fadar shugaban kasa dake Abuja, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

Kamar yadda malami yace, kudaden da aka samo an yi amfani dasu a sassa da yawa da suka hada da tattalin arziki har da fatattakar fatara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Karin bayani na nan tafe…

Asali: Legit.ng

Online view pixel