2023: Tinubu Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

2023: Tinubu Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

  • Damar Bola Tinubu, mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC na lashe zaɓe mai zuwa na fuskar barazana
  • Wasu shugabanni, kusoshi da mambobin APC na barin jam'iyyar bisa wasu burikansu da suka yi hannun riga da jagorancin jam'iyya mai mulki
  • APC a jihar Ribas ta fara tangal-tangal biyo bayan sauya shekar jiga-jiganta a lokuta da dama gabanin zaɓen 2023

Rivers - Shugaban jam'iyyar APC a gunduma ta 16 dake ƙaramar hukumar Obio/Akpor a jihar Ribas, Achinike Owhomka, ya jagoranci wasu jiga-jigan jam'iyyar sun koma SDP.

A ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba, 2022, yan siyasan suka ayyana shiga jam'iyyar SDP a Ofishin Sanata Mognus Abe dake Freedom House, GRA Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Masu sauya sheka zuwa SDP a Ribas.
2023: Tinubu Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar Hoto: Rivers Mirror
Asali: Facebook

Jiga-jigan siyasan sun samu tarba hannu bibbiyu daga ɗan takarar gwamna a inuwar SDP, Sanata Mognus Ngei Abe.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Kwankwaso Ya Dira Patakwal Wurin Gwamna Wike

Meyasa suka ɗauki matakin sauya sheƙa?

Masu sauya shekar sun ce sun yanke wannan shawara ne bayan gano Sanata Magnus Abe ne ya fi dacewa ya ja ragamar jihar Ribas, don haka babu zabin da ya wuce kowa ya haɗa hannu da shi har ya kai ga nasara a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsu, idan har Sanatan ya ɗare kujerar gwamnan jihar Ribas, zai kafa gwamnati mai nagarta da zata amfanar da kowa, kamar yadda Ribas Mirror ta rahoto.

Da yake nasa jawabin bayan karban yan siyasan, ɗan takarar gwamna a SDP, Sanata Magnus Abe, yace ba za'a nuna musu banbanci ba, sun zama ɗaya da kowa.

Bugu da ƙari, ya ce za'a ba kowanensu damar da zai ba da gudummuwarsa yayin da jam'iyyar SDP ta kama hanyar zuwa gidan gwamnatin Ribas a zaɓen da ke tafe.

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

A wani labarin kuma Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Jaddada Cewa Basu Ba Kamfen Atiku

Tsagin gwamna Wike sun cimma matsaya a taron da suka gudanar a jihar Legas, sun kuma amince da raɗa wa tawgarsu sunan "Tawagar gaskiya."

Gwamna Wike, da gwamnonin G5 da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun ce ba zasu yi wa Atiku yaƙin neman zaɓe ba har sai an samu dai-daito a jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel