Abin da Tinubu Ya Gani, Ya Dauko Shettima a Matsayin Abokin Takaransa – Kungiya

Abin da Tinubu Ya Gani, Ya Dauko Shettima a Matsayin Abokin Takaransa – Kungiya

  • All Progressives Congress (APC) Rebirth Group tayi bayanin silar dauko Kashim Shettima a 2023
  • Aliyu Audu yace Sanata Kashim Shettima ya tabuka abin a yaba a lokacin da ya yi Gwamnan Borno
  • Audu shi ne shugaban kungiyar, ya yabi yadda Shettima da Babangana Zulum suka kawo cigaba

Abuja - Kungiyar All Progressives Congress (APC) Rebirth Group tayi bayanin abin da ya kawo Kashim Shettima ya samu takara a jam’yyar APC.

Vanguard ta rahoto shugaban kungiyar, Aliyu Audu yana cewa ayyukan da Sanata Kashim Shettima ya yi a Borno ya sa Bola Tinubu ya tafi da shi.

Alhaji Aliyu Audu yake cewa Kashim Shettima ya tabuka abin kirki a lokacin da ya yi gwamnan jihar Borno tsakanin Mayun shekarar 2011 da 2019.

A cewar shugaban kungiyar, Shettima ya yi kokari wajen hada-kan mutane mabanbantan addinai da kabilu yayin da ake rikicin Boko Haram.

A wancan lokaci ‘yan ta’addan Boko Haram sun addabi yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Kungiyar tace hakan bai hana Shettima yin aiki ba.

Audu ya yi wannan bayani a lokacin da sashen siyasa na Politics Hub na jaridar Vanguard ya tattauna da shugaban kungiyar magoya bayan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A cewarsa, ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar ya yi kokarin bunkasa bangaren kiwon lafiya da na ilmi alhali al’umma na cikin halin dar-dar.

Jawabin Aliyu Audu

“Kashim Shettima a bangare guda shi kadai ne Gwamnan da ya yi mulki a tsakiyar ta’addanci, ya iya hada-kan Borno duk da sabanin addini da kabilanci.
Ya bunkasa bangaren ilmi da kiwon lafiya a bangarori dabam-dabam da mutane ba su taba tunanin hakan zai yiwu a lokacin da ake tsakiyar ta’addanci ba.”

- Aliyu Audu

Jagoran na APC Rebirth Group yace Sanata Shettima ya kawo Farfesa Babagana Zulum wanda ya gaje shi a matsayin Gwamna lokacin da ya bar gadon mulki.

An rahoto Aliyu Audu yana mai cewa duk jihohin da ke yankin Arewacin Najeriya babu jihar da ta samu cigaba kamar Borno a cikin shekaru 11 da suka wuce.

Tikitin Musulmi-Musulmi

A cewar Asiwaju Bola Tinubu, kun ji labari wadanda suke babatu saboda ya dauko Kashim Shettima, sun nemi su zama abokan takararsa a zabe mai zuwa.

Amma Tinubu bai kama sunan wadanda suka sa ran zama ‘yan takaran mataimakin shugaban kasa a APC ba, ya yi wannan bayani ne da ya zauna da CAN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel