Zan Bar Najeriya Cikin Aminci, Buhari Ya Tabbatarwa ’Yan Najeriya

Zan Bar Najeriya Cikin Aminci, Buhari Ya Tabbatarwa ’Yan Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, zai tabbatar da alkawarin da ya dauka na wanzar da tsaro a Najeriya
  • Buhari ya halarci wani taro a Abuja, ya yi kira ga 'yan Najeriya da suke girmama lamarin sojojin kasar nan
  • 'Yan Najeriya na kokawa kan mulkin Buhari, yayin da shi kuwa yake kara bayyana nasarorin da ya cimma

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jaddada manufarsa ta barin Najeriya cikin aminci a yayin da zai mika mulki ga sabon shugaba a 2023.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba a taron kaddamar Emblem Appeal a shirin bikin tunawa da sojoin kasar nan na 2023 da aka gudanar a Abuja.

Buhari ya kuma sanar da ba da tallafin N10m ga gidauniyar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: CAN za ta yi wata zama da 'yan takarar shugaban kasa saboda wasu dalilai

Buhari ya yi alkawarin inganta tsaro kafin ya sauka a mulki
Zan Bar Najeriya Cikin Aminci, Buhari Ya Tabbatarwa ’Yan Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya kuma yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su tallafawa tsoffin sojoji tare da ba da agaji ga iyalan jami'an da suka rasu don tunawa dasu da kuma yaba jajircewarsu da gudunmawa ga kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taron wanda ya biyo bayan zaman majalisar zartaswa ta kasa (FEC), ya samu halartar manyan kasar nan, ciki har da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Hakazalika, shugaban majalisa, Ahmad Lawan ya hallara, ministoci, jami'an soji da sauran masu kula da tsaron kasar nan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

'Yan Najeriya da dama na ci gaba da kuka da yadda gwamnatin Buhari ke tafiya, musamman kan harkokin da suka shafi tsaro da tattalin arziki.

Buhari ya sha yin alkawarin samar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya, amma ana ci gaba da samun hare-haren 'yan ta'adda.

Buhari ya fusata, ya yi Allah wadai da labarin kashe basaraken Imo

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ‘Dan Majalisa Ya Fadi Ana Tsaka da Ralin Tinubu, Ya Rasa Ransa

A wani labarin kuma, shugaba Bubari ya bayyana kaduwa da shiga tashin hankali bayan samun labarin kashe wani basaraken jihar Imo a makon nan.

Buhari ya umarci jami'an tsaro da su gaggauta shawo kan matsalar tsaro a yankin, kuma su kamo wadanda ake zargi da aikata wannan kisan gilla.

A bangare guda, ya mika ta'aziyya ga 'yan uwa da dangin mamacin da kuma yin addu'ar neman waraka ga wadanda suka jikkata a harin da aka kai kan sarkin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel