Kungiyar Kiristocin CAN Za Tu Tattauna da Tinubu, Atiku da Obi Ranar Laraba

Kungiyar Kiristocin CAN Za Tu Tattauna da Tinubu, Atiku da Obi Ranar Laraba

  • Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) za ta tattauna da 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun LP, APC da PDP
  • Tuni aka fara tattaunawa da wasu 'yan takarar jam'iyyu, sun bayyana abubuwan da suka shirya yiwa Najeriya
  • Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023 mai zuwa, tuni an fara gangamin kamfen

Abuja - Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa daga dukkan jam'iyyu don tattauna makomar kiristoci a Najeriya bayan zaben 2023.

Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ya ce kasar nan na fuskantar kalubalen ci gaba da shugabanci, don haka akwai bukatar jin manufofin 'yan takarar da son gaje Buhari.

Ya daura alhakin matsalolin Najeriya ga rashin daidaito a kudin tsarin mulkin kasar da kuma hanyar tafiyar da lamuranta.

Shugaban na CAN ya bayyana hakan ne ganawar farko da 'yan takarar shugaban kasa na 2023 da kungiyar kiristoci ta shirya a Abuja ranar Talata, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya fadi hanyar da zai bi wajen biyan da ake bin Najeriya idan ya gaji Buhari

Kungiyar ta shirya zama ne da 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 don tattauna manufofinsu da kuma yadda za a wanza da zaman lafiya, adalci da daidaito ga kowa.

CAN ta hada zama da 'yan takarar shugaban kasa
Kungiyar Kiristocin CAN Za Tu Tattauna da Tinubu, Atiku da Obi Ranar Laraba | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban na CAN ya bayyana cewa, kungiyar ta jima tana bibiya tare da duba ga matsalolin da suka hana ruwa gudu a fannin zaman lafiya da ci gaba a kasa, kana ta samar da wata mafita da za ta warware matsalolin.

CAN ta tattauna da 'yan Najeriya, ta gano matsaloli da mafita

Okoh ya bayyana cewa, CAN ta tattauna da mutane da dama a Najeriya, ciki har da wadanda ba mabiya addinin kirista ba a bangarori daban-daban na kasar, kuma ta hada mafitar da ta samu a rubuce.

A cewarsa, manufar wannan zama ita ce ta tabbatar dukkan 'yan takarar shugaban kasa sun fahimci abin da ke damun kiristocin Najeriya tare da samar da hanyoyin magance su.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Kudu ya gayyaci sarkin Kano, Buhari da saruan jiga-jigai don kaddamar aiki a jiharsa

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AA, Hamza Al-Mustapha ya ce, manyan matsalolin Najeriya su ne; cin dunduniya a fannin rashin tsaro da tattalin arzki.

Ya kuma bayyana cewa, wadannan matsaloli su za bi gwamnati mai zuwa, don haka Najeriya na bukatar jajirtaccen shugaba a 2023.

Za a tattauna da Tinubu, Atiku da Obi a yau

Yayin da aka fara tattaunawar tun jiya, a yau Laraba 16 ga watan Nuwamba za a ci gaba da tattaunawar, inda ake sa ran ganin dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu.

Hakazalika, Dan takarar PDP, Atiku Abubakar zai hallara, haka nan da kuma dan takarar shugaban kasa na Peter Obi, Within Nigeria ta tattaro.

Idan baku manta ba, Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na 2023.

Sai dai, zabar Shettima ya jawo cece-kuce daga CAN, ganin cewa Tinubu Musulmi ne, kuma ya zabi Musulumi a matsayin abokin takara.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Wata Jihar Arewa, Sun Yi Alkawarin Kawowa Tinubu Kuri'u Miliyan 4

Tuni CAN tace ba za ta taba amince da takarar tikitin Musulmi da Musulmi ba, kamar dai yadda APC ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel