Masu Kada Kuri’a a Jihar Zamfara Dukkansu Tinubu da Matawalle Za Su Zaba, Inji Tsohon Gwamna Yari

Masu Kada Kuri’a a Jihar Zamfara Dukkansu Tinubu da Matawalle Za Su Zaba, Inji Tsohon Gwamna Yari

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa, jama'ar jihar Zamfara a shirye suke su zabi APC a zaben badi
  • Ya kuma shawarci 'yan Najeriya da su ba da kuri'unsu ga Tinubu da sauran 'yan APC a kowace kujera a fadin kasar nan
  • Dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu ya yi kicibus da abokin hamayyarsa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar

Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul'aziz Yari ya ce, masu kada kuri'u a jihar a shirye suke su zabi dan dan takarar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.

Yari ya kuma bayyana cewa, mutan Zamfara a shirye suke su sake ba gwamna Bello Matawalle kuri'unsu a zaben na 2023, PM News ta ruwaito.

Yari ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a karamar hukumar Talata Mafara a yayin wani katafaren kamfen na sanatan Zamfara ta Yamma a yankin.

Kara karanta wannan

Kicibus: Bidiyon yadda Tinubu da Atiku suka yi gamuwar ba zata a filin jirgin sama

Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, tawagar kamfen Yari ne ya shirya gangamin karkashin shugabancin tsohon shugaban APC na jihar, Alhaji Lawal Liman.

Yari ya ce APC 'yan Zamfara za su zaba a 2023
Masu Kada Kuri’a a Jihar Zamfara Dukkansu Tinubu da Matawalle Za Su Zaba, Inji Tsohon Gwamna Yari | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku zabi APC daga sama har kasa, dodar, inji Yari

Daga nan kuma ya yi kira ga masu kada kuri'u a jihar da su yi jam'iyyar APC daga sama har kasa dodar.

A cewarsa:

"Sakamakon yakin neman zaben APC na yau a Talata Mafara ya nuna cewa mutanen Zamfara suna goyon bayan APC dari bisa dari.
"Dukkan 'yan Najeriya ya kamata su zabi APC a kowacce kujera don kawo ayyukan ci gaba masu ma'ana a kowane mataki."

A cewarsa, Tinubu da Matawalle da na shirin ayyuka masu kyau ga 'yan Najeriya da mutanen Zamfara, wadanda za su ciyar da al'umma gaba, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu da Sanata Adamu Sun Gana da Shugaba Buhari Bayan Dawowarsa Najeriya daga Landan

Yari ya kuma yabawa wadanda suka shirya gangamin kamfen din, tare da bayyana jin dadinsa da ganin irin wannan karimci da nuna goyon baya da suka yi.

Ya kuma danganta sulhunsa da gwamna Matawalle da sauran masu ruwa da tsaki na APC da tushen nasarar APC a zabe mai zuwa.

Tinubu ya gamu da Atiku a filin jirgin saman Abuja

A wata gamuwa mai ban mamaki, dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya gamu da abokin hamayyarsa daga jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Sun gamu ne a filin jirgin saman Abuja yayin da suke ci gaba da gangamin kamfen na zaben 2023 mai zuwa.

An ga Tinubu da Atiku a zaune suna tattaunawa mai nuna abota a wani bangare da tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel