Yadda Sanatan Najeriya Ya Rika Sayar da Makamai ga Jama'a
- Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ya taɓa yin sana'ar sayar da manyan makamai a matakin ƙasa da ƙasa a baya
- Kalu ya amsa cewa yana sayar da makaman ne ga duk wanda ke da kuɗin saya, amma ya bar sana'ar sakamakon buƙatar iyayensa
- Sanatan ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya kuma magantu kan zamantakewarsa da shugabannin ƙasar Afirka ta Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Tsohon gwamnan jihar Abia kuma Sanatan Abia ta Arewa a yanzu, Orji Uzor Kalu, ya gigita mutane bayan ya fito fili ya bayyana sana'ar da ya taɓa yi ta cinikin manyan makamai a matakin ƙasa da ƙasa.
Sanata Kalu ya bayyana cewa kafin ya bar sana'ar, kasuwancinsa ya wuce iyakokin Najeriya inda yake hulɗar cinikin manyan makamai daga wannan ƙasa zuwa waccan.

Source: Facebook
Arise TV ta wallafa a X cewa Kalu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake magana kan dadaddiyar dangantakarsa da tsoffafin shugabannin ƙasar Afirka ta Kudu da kuma na yanzu.
Orji Uzor Kalu ya sayar da makamai
Yayin da mai gabatar da shirin ya tambaye shi ko shi ɗan kasuwar makamai ne, Kalu ya amsa da:
"Ƙwarai kuwa, sannan na daina ne saboda..."
Da yake bayanin dalilin da ya sa ya ajiye sana'ar, ya bayyana cewa iyayensa ne suka sa shi ya dakata.
Ya ce:
“Amma iyayena, mahaifiyata da mahaifina sun zo suka ce lallai dole ne na daina sana'ar, sannan na tsaya.”
Yayin da aka tambaye shi ko ya sayar da makaman ne ga mutanen da ke da niyyar amfani da su wajen kashe mutane, Kalu ya jaddada cewa damuwarsa ita ce samun kuɗi kawai.
“A'a, a'a, a'a, a'a. Ni dai ina sayar da bindigogi ne domin in sami kuɗi, ko sun lalata abubuwa da su ko ba su lalata ba, wannan ba damuwata ba ce.”
Maganar Sanata Kalu kan Afrika ta Kudu
Kazalika, lokacin da aka tambaye shi ko ya riƙa samar da makamai ga jam'iyyar ANC yayin yaƙin kawar da nuna bambancin launin fata a Afirka ta Kudu, Kalu ya ƙana cewa bai takaita sayarwa ga ANC kaɗai ba.
Ya ce abokan kasuwancinsa sun haɗa da kowa muddin yana da kuɗin biya:
“Ni ina sayarwa ne ga duk wanda ke buƙatar saya. Idan kana da kuɗi kana son saya a D.R.C, zan sayar ma, idan kana son saya a Namibia, kana son saya...”
Da aka tambaye shi inda yake samo waɗannan makamai, sanatan ya ƙi bayyana takamaiman wuri, inda ya amsa da:
“Wannan sirrin kasuwancina ne.”
A yayin hirar, Kalu ya kuma karkata kan dangantakarsa da shugabannin Afirka ta Kudu tun daga abotarsa da tsohon shugaban ƙasar, Nelson Mandela.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa Kalu ya ce Mandela ne ya gabatar da shi ga shugabanni da dama ciki har da Thabo Mbeki da shugaba Cyril Ramaphosa na yanzu.
Jam'iyyar NDC ta caccaki Orji Kalu
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NDC ta yi wa Sanata Orji Uzor Kalu rubdugu kan yabon da ya yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu game da halin tattalin arziƙin ƙasar.
A bayanin da ya yi a baya, Kalu ya nuna cewa shugaba Tinubu ya yi ayyuka masu kyau a Najeriya kuma hakan zai saka 'yan ƙasa su sake zaɓen shi a nan gaba.
Sai dai jam'iyyar NDC ta yi masa kakkausan martani, inda ta ce maganganun Sanatan ba daidai ba ne ko kaɗan domin a cewarta 'yan Najeriya suna cikin wahala sakamakon manufofin gwamnati.
Asali: Legit.ng


