Atiku Ya Sake Maganar da ke Tada Hankalin Tinubu kan Tallafin Man Fetur

Atiku Ya Sake Maganar da ke Tada Hankalin Tinubu kan Tallafin Man Fetur

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake jaddada alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce dawo da tallafin zai taimaka wajen rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa tare da sauƙaƙa musu samun man fetur
  • Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar a ranar Litinin, tare da wani bidiyon kamfen da ya yi bayani kan tsarin tallafin da yake son dawo da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake jaddada cewa zai dawo da tallafin man fetur idan ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya yi maganganu kan rusa takarar Atiku

Atiku ya ce matakin zai taimaka wajen sauƙaƙa rayuwar ’yan Najeriya da kuma rage musu nauyin tsadar man fetur.

Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce matsayinsa kan dawo da tallafin bai sauya ba.

Atiku zai dawo da tallafin mai

A bayanin da ya yi, Atiku Abubakar ya wallafa bidiyon kamfen da ke bayanin yadda yake son dawo da tallafin man fetur, inda ya ce:

“Matsayina bai sauya ba! Zan dawo da tallafin man fetur domin sauƙaƙa rayuwa da kuma rage tsadar abubuwa ga ’yan Najeriya.”

A cikin bidiyon, wata mata da ta yi magana ta bayyana cewa ana sayar da litar man fetur a Najeriya kan sama da Naira 1,300.

Ta kwatanta farashin da na wasu ƙasashen da ke haƙar ɗanyen mai, ciki har da Libya, Iran, Venezuela, Kuwait da Saudiyya, inda ta ce jama’arsu na samun man fetur a farashi mai rahusa.

Wajen da ake sayar da mai
Mutane na shan mai a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tsarin tallafin mai na Atiku

Bidiyon ya bayyana cewa tallafin da Atiku ke shirin dawo da shi zai shafi man fetur da matatun mai na cikin gida suka samar, ba wanda aka shigo da shi daga ƙasashen waje ba.

Kara karanta wannan

Obi ya shiga wa Atiku fada kan rusa 'yan takarar ADC da kotu ta yi

An kuma ambato Atiku yana cewa matsayinsa bai sauya ba kuma ba zai sauya ba, domin zai dawo da tallafin mai.

Bayanin da ke cikin bidiyon ya nuna cewa tsarin zai taimaka wa matatun mai na cikin gida su ci gaba da aiki har sai sun kai matsayin da za su iya gudanar da ayyukansu ba tare da tallafin gwamnati ba.

Alƙawarin Atiku na baya-bayan nan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

Magana kan takarar Atiku

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Dino Melaye ya nuna bacin ransa a wata hira game da makomar takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 bayan hukuncin da kotu ta yanke.

Melaye ya bayyana cewa za su yi duk abin da ya dace da gaske domin ganin sunan Atiku Abubakar ya fito fili a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa.

Wannan martani ya biyo bayan matakin kotun ne wanda ya rusa shugabancin jam'iyyar ADC na David Mark da kuma soke dukkan matakan da suka ɗauka, ciki har da tsayar da Atiku takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng