Alaƙa Ta Fara Tsami tsakanin Majalisar Dokoki da Gwamnatin Jihar Kano
- Yan majalisar Dokokin Kano sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda Kwamishinan Labarai ke bayyana bayanan majalisa kafin lokacin da ya dace
- Lawan Hussaini Dala ya ce bai kamata kwamishinan ya riƙa magana kan batutuwan da majalisa ba ta sanar da jama’a a hukumance ba
- Majalisar ta ware ranar 11 ga Nuwamba, 2026, domin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da sabon kasafin kuɗin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano – An samu takun-saka tsakanin Majalisar Dokokin Kano da ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar.
Hakan ya biyo bayan nuna rashin jin daɗin ’yan majalisar da yadda ake fitar da bayanan da suka shafi ayyukansu.

Source: Facebook
Gargadin da majalisa ta yi wa kwamishina
Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya bayyana matsayar majalisar ne yayin zaman da aka gudanar ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026, cewar Aminiya. Dalilin da ya sa majalisar ta fusata, cewar Aminiya.
A yayin zaman, Dala ya yi korafi kan yadda Kwamishinan Labarai ke yin magana kan abubuwan da suka shafi majalisa kafin a kammala gabatar da su ga ’yan majalisar.
A cewarsa, ya kamata a mutunta tsarin da majalisar ta tanada wajen gudanar da ayyukanta, maimakon a riƙa bayyana bayanan da suka shafe ta tun kafin lokacin sanar da su.
Ya nuna cewa majalisar na da nata hanyoyin tantancewa da fitar da bayanai, don haka bai dace wani jami’in gwamnati ya yi gaban kansa wajen bayyana irin waɗannan batutuwa ba.

Source: Original
Matsayar majalisa kan kasafin kuɗin jihar
Da yake magana kan tsarin kasafin kuɗi, shugaban masu rinjayen ya tunatar da cewa gwamna ne ke da alhakin miƙa shirin kashe kuɗin gwamnati ga majalisa domin ta duba shi.
Ya jaddada cewa ba wai gabatar da kasafin kuɗin kawai ake buƙata ba, majalisar dokokin tana da hurumin yin nazari da tantance abubuwan da ke cikinsa kafin ta yanke hukuncin amincewa da shi.
Lokacin da za a gabatar da sabon kasafin
Dala ya tabbatar da cewa ofishin gwamna ya aika da takardar neman damar gabatar da sabon kasafin kuɗin jihar ga majalisar.
Bayan nazarin buƙatar, ’yan majalisar sun amince da ita tare da ayyana Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a matsayin ranar da za a miƙa daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben shekarar 2027 a matakin jiha da na Tarayya.
Majalisar Kano ta tabbatar da nadin Kwamishinoni
An ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin mutum shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar domin zama kwamishinoni.
Waɗanda aka tabbatar sun haɗa da Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya, Farfesa Sani Lawan da Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa.
Sababbin kwamishinonin sun yi alƙawarin inganta tsaro, yaɗa ilimin kimiyya da fasaha da kuma yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ba su dace ba.
Asali: Legit.ng

