Pantami na Shirin Fara Kamfen, PDP Ta Gamu da Gagarumin Koma Baya a Gombe

Pantami na Shirin Fara Kamfen, PDP Ta Gamu da Gagarumin Koma Baya a Gombe

  • Tsohon shugaban PDP a Gombe, Barr. Joel Jagafa, da tsohon SSG, Chief James Pisagih, na cikin waɗanda suka koma APC
  • Tsohon sakataren PDP na jiha, Buba Shanu, da wasu fitattun ’yan siyasa ma sun bi sahun masu sauya sheƙa
  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya tarbi waɗanda suka koma jam’iyyar, tare da tabbatar musu ba su dama da haɗin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda suka bayyana goyon bayansu ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Daga cikin waɗanda suka koma APC akwai tsohon shugaban PDP a jihar, Barr. Joel Jagafa, da tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Chief James Pisagih.

PDP ta samu koma baya a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya tare da jiga-jigan PDP da suka sauya sheka zuwa APC Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Wike zai raba biliyoyi don tabbatar da tazarcen Tinubu

Haka kuma, tsohon sakataren PDP na jiha, Buba Shanu, yana cikin fitattun ’yan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki.

Sun bayyana komawarsu APC ne a hukumance yayin wani taro da suka yi da Gwamna Yahaya a gidan gwamnatin jihar da ke Gombe.

Sauran ’yan siyasar da suka koma APC

Sauran waɗanda suka bi sahun masu sauya sheƙar sun haɗa da tsohon babban jami’in gudanarwa a Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Sunday Danlele.

Haka kuma, wani tsohon darakta da aka bayyana da suna Mista Williams, tare da wasu ’yan siyasa da dama, sun shiga jam’iyyar APC.

Hon. Ali Isa JC ne ya taimaka wajen shirya ganawar da ta haɗa waɗannan tsoffin jiga-jigan PDP da gwamnan.

Dalilin sauya sheƙarsu zuwa APC

A cikin sanarwar ya ce waɗanda suka sauya sheƙar sun bayyana amincewarsu da salon jagorancin Gwamna Yahaya.

Sanarwar ta ce sun kuma yi alƙawarin mara wa gwamnan baya, tare da bayar da gudunmawarsu wajen ƙarfafa APC da ayyukan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Okowa: Abokin takarar Atiku a 2023 ya bayyana dalilin da ya sa suka raba gari ya koma APC

Bugu da ƙari, sababbin waɗanda suka shiga jam’iyyar sun yi alƙawarin amfani da ƙwarewarsu a siyasa, tasirinsu a tsakanin al’umma da hanyoyin sadarwarsu wajen faɗaɗa tasirin APC.

Sun kuma ce za su taimaka wajen ƙarfafa tsarin jam’iyyar a matakai daban-daban, tare da wayar da kan jama’a domin samun goyon baya ga ’yan takarar APC a dukkan matakan zaɓe.

Martanin Gwamna Inuwa Yahaya

A nasa ɓangaren, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi maraba da waɗanda suka sauya sheƙar, inda ya bayyana matakin nasu a matsayin ƙarin ƙarfi ga APC a jihar.

A cewar sanarwar, gwamnan ya ce shigowar sabbin mambobin zai taimaka wajen faɗaɗa ƙarfin jam’iyyar da yawan magoya bayanta a faɗin Gombe.

Ya kuma tabbatar musu da cewa za a ba su dama su taka rawar gani a cikin jam’iyyar ba tare da nuna bambanci ba.

Gwamna Yahaya ya jaddada cewa ƙofofin APC a buɗe suke ga duk wanda yake da niyyar bin manufofinta da kuma bayar da gudunmawa wajen cimma muradun jam’iyyar baki ɗaya.

Jiga jigan PDP sun koma APC a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya tare da masu sauya sheka zuwa APC daga PDP Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Pantami zai fara kamfen

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwae jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya shirya fara fita yakin neman zabe don zaben 2027.

Farfesa Pantami ya sanar da cewa zai shiga jihar Gombe domin kaddamar da yakin neman zabe, inda ya yi godiya ga mutane daban-daban kan addu'o'in da suke yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng