Shi Ma Sheikh Gumi Ya Ɗana Yabon Gwamnatin Tinubu, Ya Magantu kan Cire Tallafi
- Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya kare manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu
- Gumi ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya zama dole bisa halin tattalin arzikin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki
- Malamin ya ce wasu muhimman alamomin tattalin arziki, ciki har da GDP da kuɗaɗen shiga na gwamnati, sun nuna ana samun ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna – Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya kare manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gumi ya bayyana cewa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka sun yi daidai da shawarwarin da masana tattalin arziki da dama za su bayar.

Source: Facebook
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin PAPShow da The Nation ta bibiya inda ya ce bai ga wani babban kuskure a manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu ba, ciki har da cire tallafin man fetur da wutar lantarki.
Ya kuma bayyana cewa wasu hukumomin ƙasa da ƙasa, ciki har da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), sun yaba da wasu daga cikin sauye-sauyen.
Gumi ya bayyana dalilin cire tallafin man fetur
Da aka tambaye shi ko Shugaba Tinubu na yin kuskure wajen tafiyar da manufofin tattalin arziki, Sheikh Gumi ya ce ba haka yake gani ba.
A cewarsa, ba wai yana cewa matakan tattalin arzikin da aka ɗauka ba daidai ba ne, domin akwai ƙalilan abubuwan da za a iya suka a tsarin manufofin gaba ɗaya.
Game da cire tallafin man fetur, malamin ya bayyana cewa matakin ya zama dole bisa yanayin tattalin arzikin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.
Ya ce:
“Cire tallafin man fetur ya kasance wani mataki da ya zama dole a aiwatar sakamakon yanayin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.”

Source: UGC
Gumi ya lissafa alamomin farfaɗowar tattalin arziki
Malamin ya ce ana samun ci gaba a wasu ɓangarorin tattalin arzikin ƙasar, inda ya kawo misalan ƙarin yawan abin da ƙasar ke samarwa (GDP), kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma rabon kuɗaɗe ga jihohi da ƙananan hukumomi.
Sheikh Gumi ya ce:
“A matakin tattalin arziki gaba ɗaya, GDP ya ƙaru, kuɗaɗen shiga na gwamnati sun ƙaru, haka kuma rabon kuɗaɗe ya ƙaru. Kusan dukkan manyan alamomin tattalin arziki suna nuna cewa tattalin arzikin Najeriya na farfaɗowa.”
Ya kuma yi nuni da yadda aka dawo da manyan ayyukan gine-gine a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, waɗanda ya ce sun kusan tsaya cak a gwamnatin da ta gabata.
Haka kuma, ya ambaci kafa sababbin jami'o'in tarayya da na jihohi a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ke nuna ci gaba.
Sheikh Gumi ya magantu kan hare-haren yan bindiga
An ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya ce wasu ’yan bindiga sun bayyana masa cewa ba sa farin cikin kashe-kashen, amma suna ganin an tilasta musu ci gaba da kai hare-hare.
Malamin ya ce ’yan bindigar na kallon rikicin a matsayin ramuwar gayya tsakanin su da al’ummomin da ke kai musu hare-hare.
Gumi ya bayyana cewa tsoron kada a kashe su idan sun ajiye makamai na daga cikin dalilan da ke hana su mika wuya.
Asali: Legit.ng

