Abokin Takaran Atiku Ya Bayyana Dalilin Rabuwa da Shi Ya Kama Layin Tinubu a APC
- Ifeanyi Okowa, ya ce ya bar Atiku Abubakar ya koma bayan Bola Tinubu ne saboda ya ga sauye-sauyen da shugaban kasar ya kawo
- Ya ce karin kudin da jihohi da kananan hukumomi ke samu ya taimaka masu wajen biyan albashi, fansho da yin ayyukan raya kasa
- Tsohon gwamnan Delta ya soki masu son dawo da tallafin man fetur, yana cewa hakan zai mayar da Najeriya baya ta fuskar tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Delta - Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya bayyana dalilan da suka sa ya bar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Ya kasance abokin takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023, amma yanzu ya koma jam'iyyar APC wajen su Bola Ahmed Tinubu.

Source: Getty Images
Abokin takarar Atiku Abubakar ya je kamfe Rivers
The Cable ta ce Ifeanyi Okowa ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a birnin Fatakwal.

Kara karanta wannan
Atiku: Dino Melaye ya bada labarin yadda kotu ta kira lauyoyin ADC karfe 11:00 na dare
Tsohon gwamnan, wanda ya kasance mataimakin Atiku a zaben 2023, ya ce ya sauya matsayinsa ne saboda ya ga manufofin Bola Tinubu a kasar.
Yake yaba wa matakan da shugaban kasar ke dauka domin magance matsalolin tattalin arziki.
A yayin da yake jawabi a babban birnin jihar Rivers ga magoya bayan APC, Okowa ya ce:
“Dukkanku kun san cewa a shekarar 2023 ina cikin wata tafiya ta siyasa daban, amma yanzu na ga haske, kuma na ga abin da Shugaba Tinubu yake yi wa Najeriya.”
Ifeanyi Okowa ya kare sauya-shekarsa zuwa APC
Okowa ya kara da cewa matakin da ya dauka na komawa APC shi ne abin da ya yi imani ya dace, yana mai cewa ya dade da barin jam’iyyar PDP.
‘Dan takaran sanatan ya ce ya hada kai da shugaba Tinubu wajen gina sabuwar Najeriya kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito shi yana jawabi.
Okowa ya ce shugaban kasar ya fahimci gwamnatocin baya sun lalata ginshikan tattalin arziki, don haka akwai bukatar daukar matakai masu tsauri.
“Idan an lalata tushe, ba za ka iya gina komai a kai ba. Shugaba Tinubu ya fahimci cewa gwamnatocin da suka gabata sun lalata ginshikan Najeriya.
A yau muna kan hanyar da ta dace saboda ana kokarin gyara wannan tushe.”
- Ifeanyi Okowa
Dalilin goyon bayan manufofin Bola Tinubu
Tsohon ‘dan takaran na PDP ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da Tinubu ya kawo sun taimaka wajen kara kudin da jihohi da kananan hukumomi ke samu.
A cewarsa, karin kudin da ake raba wa jihohi da kananan hukumomi ya taimaka musu wajen gudanar da ayyukan raya kasa da kuma biyan albashi da fansho.
Okowa ya ce a baya ana yawan samun korafe-korafen rashin biyan albashi da kudin fansho, amma yanzu ana biya har a yi ayyuka a jihohin kasar nan.
Okowa ya soki masu son dawo da tallafin man fetur
Sanata Okowa ya kuma yi maganar batun tallafin fetur, ya soki masu alkawarin dawo da shi idan suka karbi mulki.
A cewarsa, dawo da tallafin zai mayar da Najeriya baya, musamman ganin cewa matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka suna taimakawa wajen gyara.
Ya ce bai dace a bar mutanen da suka yi amfani da tsarin tallafin man fetur wajen raunana tattalin arzikin kasar su sake lalata makomar matasan Najeriya ba.

Source: Getty Images
Rainbow Coalition: Kungiyar su Wike ta girgiza APC
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ja hankalin wasu gwamnonin APC saboda goyon bayan da yake ba 'yan takarar jam'iyyun hamayya a jihohinsu.
Ana da labari cewa wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu ruwa da tsaki a fagen siyasar Najeriya ganin ana shirin yin doya da manja.
Ana zargin cewa tasirin Nyesom Wike ya shiga Gombe duk da ministan yana ikirarin bai san Isa Pantami ba wanda yake neman zama gwamna a PDP.
Asali: Legit.ng

