Sarki Sanusi II Ya Ware Gwamna 1 a Arewa, Ya Yaba Masa Sosai Kan Ayyukan Alheri
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana jin daɗinsa kan ayyukan da Gwamna Dauda Lawal ke gudanarwa a Zamfara
- Basaraken ya yaba da ayyukan gwamnan a fannonin ilimi, lafiya, tsaro da gine-gine yayin ƙaddamar da masallaci
- Sanusi II ya ce ya san ƙwarewar Dauda Lawal tun lokacin da yake aiki a harkar banki, kuma ya ji daɗin ganin yadda yake gudanar da mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya JI dadin ayyukan da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Basaraken ya yaba masa ne kan ayyukan raya ƙasa da yake gudanarwa a jihar, musamman a fannonin ilimi, lafiya, tsaro da samar da ababen more rayuwa.

Source: Facebook
Sanusi ya bayyana hakan ne yayin da yake babban baƙo a wajen ƙaddamar da masallacin Zawiyya da makarantar Islamiyya a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, cewar TheCable.
Sanusi ya yaba da gyaran masallacin Zawiyya
Masallacin Zawiyya na daga cikin tsofaffin cibiyoyin addinin Musulunci a Zamfara, wanda ya shahara wajen samar da malamai a fannoni daban-daban.
A yayin jawabinsa, Sarkin Kano ya ce wadanda suka san yadda tsohon ginin Zawiyya yake ne kaɗai za su iya fahimtar girman aikin da Gwamna Dauda Lawal ke yi.
Sarkin ya kuma jaddada muhimmancin kula da tsaftar masallacin da kuma tabbatar da an ci gaba da gyara shi kamar yadda ya dace.
Sarki Sanusi II ya ce:
“Ya kamata a riƙa tsaftace masallacin tare da kula da shi yadda ya kamata. Dole mu kiyaye tsafta musamman lokacin da muka zo nan, saboda masallaci wurin ibada ne kuma alama ce ta Musulunci.”

Source: Facebook
Sanusi II ya yaba da ayyukan Dauda Lawal
A yayin taron, Sanusi ya bayyana jin daɗinsa kan aikin da aka gudanar, inda ya yi addu’ar Allah ya saka wa gwamnan da alheri.
Sanusi II ya ce yana ganin ayyukan da Lawal ke yi a Zamfara a fannonin ilimi, lafiya, tsaro da gine-gine, cewar Punch.
Basaraken ya ƙara da cewa ba abin mamaki ba ne a gare shi ganin irin ayyukan da gwamnan ke yi, domin ya san shi tun lokacin da yake harkar banki.
A cewarsa:
“Ina matuƙar farin ciki da wannan aiki. Allah Maɗaukakin Sarki ya saka wa gwamna da alheri.
“Ayyukan alherin da kake yi a Zamfara a bangaren ilimi, tsaro, lafiya da ababen more rayuwa.
“Ban yi mamaki ba, domin na san gwamnan tun lokacin da yake harkar banki. Na san irin ƙwarewarsa, kuma ina jin daɗin ganin yana gudanar da irin waɗannan ayyuka a matsayin gwamna.”
Gwamna Dauda ya gayyaci Sanusi II
Tun farko, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal, ya gayyaci Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda ya jagoranci buɗe Masallacin Zawiyya da aka sabunta a Gusau.
Babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, shi ma ya halarci taron inda ya jagoranci sallar Juma’a a masallacin mai dimbin tarihi.
Wasu daga cikin masu amfani da Facebook sun yaba da aikin, yayin da wasu suka yi amfani da damar wajen sukar gwamnatin Zamfara kan matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng

