2023: APC Da PDP Sun Rasa Wasu Mabiyansu a Jihar Gombe, Sun Koma Jam’iyyar NNPP

2023: APC Da PDP Sun Rasa Wasu Mabiyansu a Jihar Gombe, Sun Koma Jam’iyyar NNPP

  • Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso ta kara samun karfi a jihar Gombe a ranar Lahadi yayin da mambobin APC da PDP suka dawo cikinta
  • Masu sauya shekar sun samu tarba daga dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar, Khamisu Mailantarki
  • Wannan karin karfi ne ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Kano

Gombe - Wasu mamabobin jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) sun sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a karamar hukumar Kaltungo da ke jihar Gombe.

Da yake tarban masu sauya shekar, dan takarar gwamna na NNPP a jihar, Khanmisu Mailantarki, da sauran jiga-jigan jam’iyyar sun taya sabbin mambobin murnar samun mafaka a jam’iyyar, jaridar Punch ta rahoto.

Kwankwaso a cikin jama'a
2023: APC Da PDP Sun Rasa Wasu Mabiyansu a Jihar Gombe, Sun Koma Jam’iyyar NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

A cewar Mailantarki, dawowar jam’iyyar a wannan lokaci babban nasara ne, yayin da ya basu tabbacin cewa za su kasance a duk wasu harkoki na siyasarsa.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Ya ce daga PDP har APC sun samu damar mulkar jihar a shekarun baya, sai dai ya yi zargin cewa basu tabuka komai ba kamar yadda al’ummar jihar suka yi tsammani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mailantarki ya bayyana cewa NNPP za ta samar da mafita da ake bukata a shekara mai zuwarahoton Blueprint.

Daga karshe ya bukaci sabbin masu sauya shekar da su tattaro mutane a wurarensu.

Dan takarar gwamnan ya ce:

“Godiya ta tabbata ga Allah kan wannan nasara da NNPP ke samu a kullun kwanan duniya. Wannan sakamakon manufofi masu inganci da jam’iyyar ta tanadar ne. wannan ne dalilin da yasa Karin mutane masu yawan gaske ke tururuwan shigowa. A tare, za mu iya sannan mu samu sabuwar jihar Gombe a 2023.”

Yakamata APC ta takawa Shettima burki game da kalamansa a kan yan takarar shugaban kasa, jam'iyyar LP

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jam'iyyar APC Na Rasa Ƙarfinta A Kudu Maso Kudu Yayin Da Ɗaruruwan Mambobinta Suka Koma PDP A Babban Jiha

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa jam'iyyar Labour Party ta kalubanci abokiyar adawarta ta APC a kan ta gargadi dan takararta da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Jam'iyyar LP ta zargi Shettima da yin kalaman tozarci ga dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi da sauran masu neman takarar kujera ta daya a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel