Dan Takarar Gwamnan PDP a Zamfara Ya Fusata, Ya Yi Kakkausan Martani Kan Hukuncin Kotu

Dan Takarar Gwamnan PDP a Zamfara Ya Fusata, Ya Yi Kakkausan Martani Kan Hukuncin Kotu

  • Dan takarar gwamnan PDP a jihar Zamfara, Dauda Lawal ya magantu bayan wata babbar kotun tarayya ta soke takararsa
  • Lawal wanda ya bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na karkatar da hankalinsa daga shirye-shirye, ya sha alwashin ci gaba da yakin neman zabensa
  • Dan takarar ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu inda ya bayyana shirinsa na daukaka kara

Zamfara - Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya sha alwashin ci gaba da harkokin kamfen dinsa duk da kotu ta soke zaben fidda gwanin da ya samar da shi, Sahara Reporters ta rahoto.

A ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba ne babbar kotun tarayya da ke zama a Gusau, babban birnin jihar ta soke zaben fidda gwanin da ya samar da Lawal a matsayin dan takarar gwamna na PDP a jihar.

Kara karanta wannan

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

Dauda Lawal
Dan Takarar Gwamnan PDP a Zamfara Ya Fusata, Ya Yi Kakkausan Martani Kan Hukuncin Kotu Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Justis Aminu Bappa ya yanke hukunci cewa jam'iyyar PDP ba za ta kasance da dan takara a zaben gwamnan 2023 ba a jihar.

Wannan shine karo na biyu da kotun ke soke zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jam'iyyar adawar a Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, Lawal ya bukaci mambobin jam'iyyar, magoya baya da jama'a da su kwantar da hankalinsu bayan soke zaben fidda dan takarar gwamnan da aka yi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada muradun Dauda Lawal ya saki a Gusau inda ya bayyana hukuncin a matsayin wata dabara na jan hankali.

Ofishin ya bayyana cewa tawagar lauyoyin Lawal za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara, yana mai nuna karfin gwiwar cewa za a yi watsi da hukuncin babbar kotun, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Sake Soke Zaben Fidda Gwanin PDP, jam'iyyar ba tada yan takara a zaben 2023 a Zamfara

Jawabin ya ce:

"Duk wadannan gagarumin shiri ne na gwamnatin jihar Zamfara, jam'iyyar All Progressives Congress reshen jihsr, da wasu masu hada kai da su don janye hankalinmu. Amma kamar kulla-kulla da dama da suke yi don ci gaba da mulki sabanin ra'ayin mutane, wannan ma ba zai cimma nasaraba da izinin Allah.
"Dauda Lawal da jam'iyyar Peoples Democratic Party suna ta samun goyon baya a fadin jihar Zamfara, kuma karara ya nauna nasara, sun yanke shawarar komawa ga wasu dabaru don janye hankalinmu daga wajen mayar da hankali ga kamfen dinmu. Amma za mu ci gaba da mayar da hankali inda muka sa gaba har sai mun ceto tare da sake gina Zamfara."

Jawabin ya kara da cewar tsarin da PDP ta bi wajen samar da Lawal a matsayin dan takararta na gwamna ya yi daidai da sabuwar dokar zabe da kuma tsarin jam’iyyar da na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Kotu za ta tabbatar ban fadi zabe ba, za a dawo min da kujera ta

Saboda haka, ya bukaci mambobin jam’iyyar da su kwantar da hankali sannan su fuskanci inda suka sanya gaba kuma kada su yi abun da ka iya tayar da zaune tsaye a jihar.

Ya bayyana cewa harkokin kamfen din zaben 2023 Za su ci gaba kamar yadda aka tsara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel