Jam'iyyar PDP Ba Za Ta Gabatar Da Dan Takara A Zaben Gwamnan Zamfara Ba, Kotun Tayi Hukunci

Jam'iyyar PDP Ba Za Ta Gabatar Da Dan Takara A Zaben Gwamnan Zamfara Ba, Kotun Tayi Hukunci

  • Tarihi ya maimaita kansa amma wannan karon a kan jam'iyyar adawa ta People's Democratic Party PDP
  • Kotu ta soke dukkan yan takaran kujerar gwamnan jam'iyyar a jihar Zamfara a zaben 2023
  • Da alamun Gwamna Muhammad Bello Matawalle da mataimakinsa za su ci banza a watan Maris

Gusau - Babbar kotun tarayya dake zamanta a Gusau, jihar Zamfara, a ranar Talata ta soke zaben fidda gwanin dan takaran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Wannan ya biyo bayan soke zaben farko da kotun tayi a watan Satumba.

Dauda Lawal-Dare ne ya lashe duka zabukan biyu.

Alkalin kotun yanzu ya bayyana cewa gaba daya jam'iyyar PDP ba zata gabatar da dan takara a zaben gwamnan jihar ba da za'a gudana a 2023, rahoton ChannelsTV.

Zaku tuna cewa a watan Satumba, kotun ta soke zaben fidda gwanin farko sakamakon karar da Ibrahim Shehu da wasu yan takara suka shigar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC: Kotu za ta tabbatar ban fadi zabe ba, za a dawo min da kujera ta

Kotun ta yi umurnin a gudanar da sabon zabe kuma Lawal-Dare ya sake lashewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dauda Lawal
Jam'iyyar PDP Ba Za Ta Gabatar Da Dan Takara A Zaben Gwamnan Zamfara Ba, Kotun Tayi Hukunci
Asali: Twitter

A riwayar TVC, hukuncin kotun ba dan takaran gwamnan kadai ya shafa ba, abin ya game da dukka sauran yan takara wata kujera a jihar.

Kotun ta ce PDP ta hakura bana saboda zaben fidda gwanin da ta gudanar cike yake da magudi da rashin gaskiya.

Fitar gwamna Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara mai ci yanzu, Muhammadu Bello Matawalle ya amfana da irin wannan hukunci na kotu a zaben 2019.

Ana saura kwana daya a rantsar da wanda ya samu nasara a zaben gwamnan jihar, Kogunan Gusau, kotun koli ta soke dukkan zabukan fidda gwanin APC a jihar.

Kotun koli ta sanar da cewa jam'iyyar PDP ta maye dukkan kujeraun da APC ta lashe a shekarar.

Kara karanta wannan

Idan akayi zabe yau, Abba Gida-Gida Zai Lashe Gwamnan Jihar Kano, Binciken Anap Foundation

Bayan danewa karagar mulki, gwamna Matawalle ya fita daga jam'iyyar PDP duk da rantsuwar da yayi a baya cewa ba zai taba yaudararta ba.

Daga bisani yayi sulhu da tsohon gwamnan jihar, AbdulAziz Yar, da kuma Sanata Kabiru Marafa.

Tinubu bai bukatar kamfe a Zamfara

Dan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Garba Marafa ya fadawa jam’iyyar APC mai mulki cewa babu yan adawa a Zamfara.

Kabiru Garba Marafa ya fadawa Bola Tinubu cewa kada ya batawa kansa lokaci wajen zuwa Zamfara Kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel