Jam'iyyar APC Ta Sake Karban Dandazon Masu Sauya Sheka Daga PDP a Sokoto

Jam'iyyar APC Ta Sake Karban Dandazon Masu Sauya Sheka Daga PDP a Sokoto

  • Duk da bai wuce 'yan watanni a fita fafatawa a runfunan zaɓe ba, PDP ta kara rashin mambobinta a jihar Sakkwato
  • Jam'iyyar APC ta karbi ɗaruruwan masu sauya sheka daga PDP a yau Lahadi, Ministan Buhari ya halarci taron
  • Alhaji Maigari Dingyadi, yace wannan tururuwar shiga APC alama ce dake nuna jam'iyyar ta yi abun alheri ga yan Najeriya

Sokoto - A ranar Lahadin nan, jam'iyyar APC a jihar Sakkwato ta ƙara samun gagarumin goyon baya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.

Jaridar Vanguard tace an sake samun rukunin dandazon mambobin jam'iyyar PDP daga mazaɓun Dundaye, Gumburawa da Gidan Bubu, waɗanda suka tattara suka koma APC duk a ƙaramar hukumar Wamakko.

APC ta sake karban mambobin PDP a Sokoto.
Jam'iyyar APC Ta Sake Karban Dandazon Masu Sauya Sheka Daga PDP a Sokoto Hoto: vanguard
Asali: UGC

Da yake jawabi a wurin taron da aka shirya, ministan harkokin rundunar 'yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, ya ayyana lamarin da nasara sakamakon ayyukan alherin da Gwmanatin APC ta kawo.

Kara karanta wannan

Buhari Na Shirin Kashe Biliyan 2 Domin Sabunta Motocin Aso Villa

Ministan yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnatin APC karƙashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta kawo ayyukan ci gaba kala daban-daban a ƙasar nan da niyyar mutane su samu walwala."
"A cikin shekaru Bakwai da suka shuɗe gwamnatin nan bata yi ƙasa a guiwa ne wajen kirkiro shirye-shiryen na musamman da zasu taka rawa a rayuwar mutane masu ƙaramin karfi a ƙasar nan."
"Saboda haka ina kira gare ku da ku ƙara karfin goyon bayanku don tabbatar da nasarar APC domin ta hanyar haka ne kaɗai zaku ci gaba da shan romon demokuraɗiyya."

Mista Dingyadi ya ƙara da cewa ganin irin lagwadar da mutane ke sha a mulkin APC ne ya ja hankalin da yawa suke tururuwar shiga jam'iyyar don ba da gudummuwarsu.

Da yake karban masu sauya shekar a hukumance, shugaban APC na jiha, Alhaji Isa Sadiq-Achida, ya ayyana jiga-jigan mutamen da ginshiƙin demokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Jami’an NDLEA na Fuskantar Barazana da Kisa daga Dillalan Kwayoyi, Marwa

Ya ƙara da rokonsu da su yi duk me yuwuwa don tabbatar da jam'iyyar ta kai ga nasara a babban zaɓen jihar mai zuwa, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Meyasa auka sauya sheka zuwa APC?

Daga cikin jiga-jigan da suka sauya shekar sun haɗa da, Alhaji Labaran Gidan-Ruwa, Hajiya Balkisu Dundaye da Malami Mai-Sojoji, a cewarsu sun bar PDP ne saboda gaza cika alƙawurranta.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Bukaci Peter Obi Ya Jingine Takara, Ya Koma Jam'iyyar PDP

Tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ta nemi ɗan takarar LP, Peter Obi ya aje takara ya marawa PDP baya a 2023.

Kakakin PCC, Sanata Dino Melaye, yace Obi ba zai iya cin nasara a.zaben da ke tafe ba saboda a iya yanki ɗaya ya yi suna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel