Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

  • Duk da cewa Peter Obi, ba shi da abin da wasu masana kimiyyan siyasa ke kira 'structure', dan takarar shugaban kasar na LP yana barazana ga wasu
  • Daya daga cikin wadannan mutanen da suka san cewa an samu canji a siyasar Najeriya akwai jiga-jigan jam'iyyar APC
  • Mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar APC, Hannatu Musawa, ta ce ta yi wu Obi ya ci Benue, Plateau da Taraba a 2023

Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Peter
2023: Mataimakin Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai yiwuwar Peter Obi ya ci Plateau, Benue da Taraba

A yayin da ta ce a arewa ne za a ci zabe ko a sha kaye, Musawa ta ce akwai yiwuwar tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ci jihohi kamar Benue, Plateau da Taraba.

Musawa ta ce:

"A arewa za a ci zabe ko a sha kaye. Wannan shine gaskiya. Ko ana so ko ba a so.
"Tanadin kundin tsarin mulkin kasa da dokar zabe ba ta tsaya bane kawai ga miliyoyin mutane su fito su maka tattaki. Kana bukatar wani adadin kuri'u daga wani adadin jihohi.
"... bana tunanin zai ci wani jiha a arewa sai dai Benue, Plateau da, wata kila, Taraba, da ake bukata don cin zaben kasa..."

'PDP Ta Gina Bandaki Guda 3 Da Naira Miliyan 12 Da Ta Samu Yayin Sayar Da Fom'

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

Amfani da kimanin naira miliyan 12 don gina bandaki guda uku ya kara ta'azzara rikicin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, The Punch ta gano a ranar Talata.

An ce an samu kudin ne daga sayar da fom a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar don zaben shekarar 2023.

Duk da cewa wani jami'i na jam'iyyar ta PDP na kasa aka bawa kwangilar, majiyoyi sun ce lamarin ya janyo rabuwar kai a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel