PDP a dabaibaye take da kitimurmura, ba ta da mafita nan da zabe mai zuwa, inji APC

PDP a dabaibaye take da kitimurmura, ba ta da mafita nan da zabe mai zuwa, inji APC

  • Jigon jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga halin da PDP ke ciki, inda yace sam jam'iyyar ba za ta tsinana abin kirkiri ba
  • Jam'iyyar PDP na fuskantar rikicin cikin gida tun watan Mayun bana, lokacin da Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa na 2023
  • Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da musayar miyau tun bayan buga gangar siyasa a shirin zabe mai zuwa na badi

Jihar Legas - Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC ya bayyana irin halin matsi da rikici da jam'iyyar adawa ta PDP ke ciki a halin yanzu, The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hasashensa game da makomar PDP a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Legas a ranar Laraba, inda yace ba zai yiwu PDP ta warware damuwar da take ciki ba nan da zaben 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: NEC Ta Yi Magana Kan Hukunta Wike, Ortom Da Wasu

APC ta caccaki PDP kan halin da take ciki na rikicin cikin gida
PDP a dabaibaye take da kitimurmura, ba ta da mafita nan da zabe mai zuwa, inji APC | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Idan baku manta ba, PDP ta tsunduma cakwalkwalin rikici ne tun a watan Mayu, lokacin da Atiku Abubakar ya zama dan takarar ta na shugaban kasa.

Nyesom Wike, gwmanan jihar Ribas ne tushen matsalar, wanda kuma shine yazo na biyu a zaben fidda gwanin da PDP ta aiwatar na dan takarar shugaban kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike dai ya ki ba da hadin kai ga Atiku, kuma yana tare da wasu gwamnoni masu ra'aui irin nasa na adawa da yadda PDP ke tafiyar da shugabancinta.

Halin da PDP ke ciki, inji hasashen Morka

Kakakin na APC ya bayyana PDP a matsayin jam'iyyar da ke cikin rikicin cikin gida, kuma hakan babban kalubale ne gareta, NaijaNews ta tattaro.

A cewarsa:

"PDP ta dabaibaye ciki cakwalkwalin rikici wanda bana tunanin za su warware nan da zabe mai zuwa. Kusan da kansu suka tsoma kansu cikin wannan rikici saboda haka abin yake a al'adarsu, rarrabuwar kai na cikin gida a cikin jam'iyyar."

Kara karanta wannan

2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

Ya kuma yi tsokaci game da kadan daga shirin Bola Tinubu, dan takararsu na shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Ya ce Tinubu zai yi kokari wajen tabbatar da rage tafiye-tafiyen duba likita zuwa kasashen waje matukar 'yan Najeriya suka bashi dama ya gaji Buhari a zabe mai zuwa.

Kotu Ta Bada Umarnin Sake Zaben Fidda Gwani Na APC a Mazabar Sanatan Nasarawa Ta Yamma

A wani labarin, babban kotun tarayya da ke zama a birnin Lafia ta jihar Nasarawa ta rushe zaben fidda gwanin sanatan mazabar Nasarawa ta Yamma kana ta ba da umarnin a gaggauta sake yin sabo, Tribune Online ta ruwaito.

Mai shari'a Nehezina Afolabi ne ta bayyana hakan a hukuncin da ta yanke kan karar da Mr Labaran Magaji ya shigar kan kalubalantar jam'iyyar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin.

A cewar mai shari'a, jerin sunayen deliget da suka kada kuri'a a zaben na ranar 4 ga watan Yunin 2022 na bogi ne, don ba Mr Shehu Tukur tikitin takara ya rushe bisa umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel